in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Neymar ya nuna sha'awar buga gasar Olympic
2016-03-16 13:46:18 cri
Dan wasan gaban Barcelona Neymar, ya bayyana sha'awar sa ta shiga jerin 'yan wasan da za su bugawa Brazil kwallon kafa a gasar Olympics ta birnin Rio dake tafe cikin watan Agustan wannan shekara.

Wata jaridar kasar Brazil ta rawaito babban jami'in tsare-tsaren kungiyar kwallon kafar kasar Gilmar Rinaldi, na cewa duk da kasancewar kungiyar Barcelona ta nuna turjiya game da hakan, yana fatan daga karshe za a cimma matsaya game da baiwa dan wasan damar buga wasa a yayin gasar ta Olympic.

Bisa ka'idojin gasar Olympic dai, ko wace kungiya na da damar sanya 'yan wasa uku da shekarun su suka haura 23 cikin tawagar su, wanda hakan ya baiwa Brazil damar shigar da Neymar mai shekaru 23, da Willian na Chelsea da kuma Miranda dake bugawa Inter Milan wasa cikin tawagar ta.

Za dai a buga gasar wasannin Olympic dake tafe ne tsakanin ranekun 4 zuwa 20 ga watan Agusta mai zuwa, kimanin makwanni 6 bayan kammala Copa America a kasar Amurka. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China