in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kwallon kafar Najeriya zata dawo da tsoffin yan wasanta
2016-03-02 15:35:32 cri

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta fara tattaunawa da tsohon mai tsaron gidan Super Eagles Vincent Enyeama, da tsohon mai tsaron bayan kungiyar Emmanuel Emenike, domin duba yiwuwar dawo dasu kungiyar ta Super Eagles.

Mai rikon kociyan kungiya ta Super Eagles, Samson Siasia ya fada a Abuja cewar, manufar wannan yunkuri shine, domin tattaro kwararrun 'yan wasan don tunkarar wasannin da zata buga da Masar.

Najeriyar zata buga muhimmin wasan share fagen shiga gasar wasannin cin kofin nahiyar Afrika AFCON, inda zata fafata da kungiyar wasa ta Pharaohs ta kasar Masar cikin wannan wata.

Siasia, yace NFF na cigaba da lalibo hanyoyin da zasu baiwa kungiyar wasan nasara, don haka ta fara daukar matakan da suka dace domin samun nasarar maido da 'yan wasan zuwa kungiyar.

Kociyan wanda ya taba lashe kyautar azurfa a gasar Olympic, ya fada cewar baya cikin firgici a yunkurin doke kungiyar wasan ta Masar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China