in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala saida tikitin wasan Brazil da Uruguay
2016-03-02 15:34:44 cri
Rahotanni daga kasar Brazil na cewa tuni aka kammala saida dukkanin tikitin wasan share fagen buga gasar kwallon kafa ta duniya, takanin kasar Brazil da Uruguay, wasan da ake fatan buga shi nan gaba cikin wannan wata a filin wasa na Pernambuco dake birnin Recife. Wasan dai zai kasance na 5 cikin jerin wasannin share fagen cin kofin duniya na shekarar 2018 da za a gudanar a kasar Rasha.

Hukumar kwallon kafar kasar Brazil ta ce ta an saida dukkanin tikiti 44, 739 da aka tanada domin kallon wannan kasaitaccen wasa, wanda ake sa ran zai kunshi 'yan wasa irin su Luis Suarez na Barcelona, wanda cizon da ya yiwa mai tsaron bayan kasar Italiya Giorgio Chiellini a gasar cin kofin duniya na shekarar 2014 ya sa aka dakatar da shi daga buga wasanni 9.

Yanzu haka dai Uruguay ce ta biyu da maki 9, inda take biye da Ecuador dake matsayin farko a jerin kungiyoyin da za su wakilci nahiyar kudancin Amurka a gasar ta duniya, yayin da kuma Brazil ke biye da maki 7 a matsayi na 3.

Ana sa ran a ranar Alhamis kocin Brazil Dunga, zai fitar da sunayen 'yan wasan da za su bugawa kungiyar ta sa wasan na gaba. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China