Hukumar kula da wasan kwallon kafan kasar NFF ce ta sanar da hakan a ranar Litinin din data gabata, tace kimanin 'yan wasan 40 ne kocin horas da 'yan wasan Florence Omagbemi ya gayyata domin shiga shirin bada horon wanda za'a gudanar a Abuja.
Najeriya, wacce ta samu nasarar zama zakara har sau 7 a wasnnin mata a nahiyar, zata kara ne da takwarorinta na kasashen Senegal da Guinea a watan Maris, da kuma ranakun 4 da 12 na watan Aprilu.
Za'a gudanar da wasannin cin kofin Afrika na mata ne na shekarar 2016 a Jamhuriya Cameroon a watan Nuwamba.(Ahmad Fagam)