in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara koyar da Sinanci a jami'ar Mozambique
2016-02-19 11:01:33 cri

A jiya Alhamis ne aka gudanar da bikin fara koyar da harshen Sinanci a kwalejin Confucius ta jami'ar Mondlane, da ke Maputo, babban birnin kasar Mozambique. Yanzu za a rika koyar da harshen na Sinanci cikin tsarin karatun jami'ar na tsawon shekaru 4.

A jawabinsa yayin bikin, jakadan kasar Sin dake kasar Mozambique Su Jian ya bayyana cewa, bullo da shirin koyar na harshen Sinanci a jami'ar Mondlane ya nuna cewa, hadin gwiwar al'adu da ilmi da musayar masana dake tsakanin sassan biyu ya shiga wani sabon matsayi, kana zai taimaka wa daliban kasar su kara fahimtar al'adun kasar Sin da na kasashen Asiya, tare da kara karfafa cudanyar harkokin ilimi dake tsakanin Sin da Mozambique. Ban da haka kuma zai taimaka wa Sinawa su kara fahimtar kasar Mozambique, ta yadda za a ciyar da dangantakar dake tsakanin sassan biyu a fannonin siyasa da diplomasiyya da tattalin arziki da kuma al'adu gaba.

Rahotanni na cewa, sama da daliban jami'ar Mondlane 200 ne suka nuna sha'awarsu ta koyon harshen na Sinanci, a karshe aka zabi 30 daga cikinsu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China