Wannan kiran na hadin gwiwa ne tsakanin kungiyar hada kan kasashen Afrika AU, da MDD, da kungiyar tarayyar turai EU, da kuma kungiyar kasashe masu magana da Faransanci IOF.
Sanarwar ta bayyana cewar, kungiyoyin suna ci gaba da bibiyar al'amurran dake wakana a kasar mai fama da rikici, musamman game da zaben kasar dake tafe.
Kungiyoyin hudu sun dauki batun zaben kasar da muhimmanci, domin ganin an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali, wanda ake sa ran zai kasance zakaran gwajin dafi wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasar.
Sanarwar ta ce kungiyoyin sun bukaci masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar congo da su yi biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, don tabbatar da yin zaben cikin nasara, da samun dauwamamman zaman lafiya da kuma kafuwar tsarin demokuradiyya a kasar.
Kaza lika, kungiyoyin hudu sun bukaci bangarorin dake hamayya da juna a DRC, da su warware duk wata takaddama ta hanyar bin ka'idojin shari'a.(Ahmad Fagam)