in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wajen Sin ya bayyana manufofin Sin kan batun nukiliya a yankin Koriya
2016-02-13 13:03:04 cri

A ran 12 ga watan nan na Fabarairu ne ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya amsa tambayoyi daga kamfanin dillancin labarai na Reuters, game da manufofin kasar Sin kan harkokin yankin Koriya a binirn Munich na kasar Jamus.

Cikin tsokacin nasa, Mr. Wang ya ce kasar Sin na kusa da yankin Koriya, tana kuma daukar babban nauyi na kiyaye zamantakewa a yankin, don haka take tsayawa tsayin daka kan wasu manufofinta dake shafar harkokin yankin Koriya. Na farko cikin wadannan manufofi shi ne, kin amincewa da kasancewar makamashin nukiliya a yankin, kirar gida ko wanda za a sayo daga ketare, a kasar Koriya ta Arewa ko a kasar Koriya ta Kudu.

Na biyu kasar Sin ba za ta amince da a warware matsalar yankin ta hanyoyin yake-yake ba, kasancewar hakan zai haddasa karin barazana a yankin. Na uku ya kamata a tabbatar, da kuma kiyaye tsaron kasar Sin yadda ya kamata.

Bugu da kari, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da kasashen duniya, wajen ciyar da yunkurin hana yaduwar makamashin nukiliya a yankin Koriya gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China