in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan Cote d'Ivoire Gervinho ya koma kulub din Chinese Super League
2016-02-02 14:59:03 cri

Dan wasan kwallon kafa na kasar Cote d'Ivoire Gervais Yao Kouassi, da aka fi sani da Gervinho, ya bar kulub dinsa na AS Roma inda ya koma kulub din kwallon kafan super League na kasar Sin, kamar yadda kulun din na Chinese Super League ya sanar a ranar Talata.

Sai dai sabon kulub din wanda ke yankin Qinhuangdao a arewacin gundumar Hebei, bai yi cikakken bayani ba kan kwangilar da aka kulla tsakaninsa da Gervinho.

Gervinho ya shedawa 'yan jaridu cewar yana sha'awar komawa Qinhuangdao ne, wanda daya ne daga cikin wuraren da aka gudnar da gasar wasannin Olympic a shekarar 2008, inda kasar sa Cote d'Ivoire ta sha kashi a hannun Najeriya da ci biyu da nema a zagayen kusa da dab da na karshe a wasannin Olympic.

Dan wasan wanda ya samu nasarar lashe kyautar shahararran dan wasan kwallon kafa na Cote d'Ivoire har sau biyu, ya taba taka leda a kulob din Beveren na kasar Belgium a shekarar (2005-2006), da kuma Le Mans na Faransa a shekarar (2007-2008). Ya kuma taba jagorantar Lille a gasar wasannin ta kasar Faransa a (2009-2010), sannan ya shafe shekarun 2010-2011 a gasar wasanni ta Premier League a Arsenal kuma ya koma AS Roma a shekarar 2013.

Gervinho ya taka leda a gasar cin kofin nahiyar Africa har karo 5, kuma ya taimakawa kulub dinsa lashe kambi a wasannin shekarar ta 2015 inda ya zara kwallaye 4 cikin raga.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China