in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya yi bayani kan manufar kasar Sin game da yankin Gabas ta Tsakiya a hedkwatar AL
2016-01-22 10:49:50 cri

A yammacin jiya Alhamis ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ya ke ziyarar aiki a karo na farko a kasashen Larabawa a wannan shekara ya yi bayani a hedkwatar kungiyar hada kan kasashen Larabawa AL dake Alkahira kan manufofin da kasar Sin take aiwatarwa, inda babban sakataren kungiyar AL Nabil el-Araby da firayin ministan kasar Masar Ishmael da wakilan kasashen kungiyar AL da ma'aikatan kungiyar AL da jami'an gwamnatin kasar Masar sama da dari biyu ne suke saurari jawabin nasa a babban dakin taron kungiyar.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, "Yankin Gabas ta Tsakiya wuri ne mai ni'ima, amma abun bakin ciki shi ne, a halin da ake ciki yanzu, al'ummomin kasashen yankin suna fama da yake-yake, don haka ana fatan za su hanzarta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali don kubutar da kansu daga wannan mawuyacnin hali da yankin ke fuskanta. ko shakka babu kasashen yankin za su cimma burinsu bisa kokarin da suke yi ta hanyar tattaunawar siyasa da kuma neman samun ci gaban tattalin arziki."

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, tattaunawa ita ce hanya mafi a'ala ta cimma fahimtar juna, kuma muddin ana bukatar a warware matsalolin da al'ummomin suke fuskanta, wajibi ne a gaggauta raya tattalin arziki, ban da haka kuma, wajibi ne kasashen yankin su zabi hanyar da ta dace da yanayin da su ke ciki. Ya ce: "Dole al'ummar kasar su zabi hanyar bunkasuwar kasarsu, bisa tarihi da al'adu da matsayin ci gaban tattalin arzikin kasar."

Shugaba Xi ya jaddada cewa, batun Palestinu batu da ke jawo hankalin kasa da kasa, saboda rikice-rikicen da ke aukuwar a yankin Gabas ta Tsakiya, ya ce, ya kamata kasashen duniya su taimaka wajen sa kaimi kan shawarwarin shimfida zaman lafiya da aiwatar da yarjejeniyoyin zaman lafiya da aka cimma bisa adalci.

Shugaba Xi ya ce, "Gwamnatin kasar Sin za ta samar da taimakon kudin RMB yuan miliyan 50 ga Palestinu domin kyautata zaman rayuwar Palestinawa, kuma za ta goyi bayan Palestinu kan aikin gina tashar samar da lantarki ta hanyar yin amfani da makamashin hasken rana."

Kazalika, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wasu hakikanan matakai game da manufofin da kasar Sin take aiwatarwa kan yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin tana fatan hada kai da kasashen yankin, ta yadda za su ci gajiyar shirin nan na "ziri daya da hanya daya", ta yadda zai taimaka wajen cimma burin shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, kuma za a taimaka wajen neman samun ci gaban tattalin arziki, musamman ma wajen raya masana'atu dake yankin. Shugaba Xi ya ce, "Manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa sun fi mai da hankali kan moriyar al'ummomin kasashen yankin Gabas ta Taskiya, kasar Sin ba ta goyon bayan wani shamaki wajen daidaita matsalar yankin, kamata ya yi a gudanar da shawarwari tsakanin kasashen kai tsaye, kana a rungumi shirin nan na "ziri daya da hanya daya" tare, ta yadda za a samu moriyar juna yadda ya kamata."

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, ya kamata a kara kyautata hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa, musamman ta fuskar hadin gwiwar man fetur da iskar gas.

A bangaren nasa, babban sakataren kungiyar hada kan kasashen Larabawa Nabil el-Araby ya bayyana cewa, ziyarar shugaban kasar Xi Jinping a wannan karon ta zo dai-dai da cikon shekaru 60 da kulla huldar diflomasiya tsakanin kasar Sin da kungiyar AL, kana, ziyarar za ta bude wani sabon shafi kan hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu. Ya ce, "Shugaba Xi, ina fatan ka fahimci irin kalubale da rikice-rikice da yankin ke fuskanta, don haka kasashen Larabawa suna bukatar goyon bayan kasar Sin kwarai, musamman ma Palestinu don ganin al'amura sun daidaita a yankin baki daya. Kuma daukacin kasashen Labarawa suna jinjinawa matsayin da kasar Sin ta dauka, sannan ka cika alkawarinka. ina kara maka maraba da zuwa hedkwatar kungiyarmu, ziyararka za ta kara ciyar da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa gaba yadda ya kamata."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China