in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Saudiya sun yanke shawarar kafa kwamitin ba da shawara kan dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu
2016-01-20 20:19:04 cri
A yau ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Saudiya tare da shugaban kasar ta Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Saudiya Adel al-Jubeir a babban birnin kasar, Riyadh.

Bayan ganawarsu, ministocin biyu sun sanar da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sarkin Salmam Bin Abdulaziz Al Saud na Saudiya sun amince su kafa wani kwamitin musamman da zai jagoranci yadda za a daidaita hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu a fannoni daban daban.

Wang Yi ya ce, ziyarar Xi Jinping a kasar Saudiya na da muhimmiyar ma'ana cikin tarihin dangantakar dake tsakanin Sin da Saudiya, kuma wani muhimmin sakamakon da aka samu shi ne, an tsai da kudurin kafa tsarin dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu. Sa'an nan ya ce, kafa kwamitin ba kawai ya nuna nasarar da aka cimma a sakamakon ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping ya kai a kasar ta Saudiya ba, haka kuma, ta kasance muhimmin mataki wajen kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, lamarin da zai taimaka wa kasashen biyu wajen habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban. Kaza kila, ma'aikatun kasashen Sin da Saudiya za su ci gaba da tattaunawa kan yadda za a kafa kwamitin, domin aiwatar da shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma cikin hadin gwiwa yadda ya kamata.

A nasa bangaren, Adel al-Jubeir ya ce, ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Saudiya na da muhimmiyar ma'ana,inda a yayin ziyarar tasa an tsai da kudurin kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, sannan aka kafa wani kwamiti na musamman domin ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu gaba, lamarin da ya bude wani sabon shafi na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China