in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharihi: Ziyarar shugaban kasar Sin za ta taimakawa shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya
2016-01-19 14:07:27 cri

Bayan da shugaban kasar Sin mista Xi Jinping ya tashi daga kasar Sin a ranar Talatar nan domin fara ziyara a kasashen Saudiya, Masar, da Iran, jaridar People's Daily ta kasar Sin, ta wallafa wani sharhi mai taken " Ziyarar ta farko da shugaban kasar Sin ya yi a shekarar 2016 za ta taimakawa kokarin da ake na shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya".

Cikin sharhin, an ce, a zamanin da ya zuwa yanzu, hanyar siliki ta hada kasar Sin da yankin gabas ta tsakiya. Wannan hanya tana tare da ma'ana mai zurfi, wadda ta kunshi ra'ayi na kiyaye zaman lafiya, da hadin gwiwa, da bude kofa, da hakuri da juna, da koyon fasahohin juna, da amfanar juna, da dai sauransu. Wadannan ra'ayoyi an riga an gaje su daga kaka da kakani, don ci gaba da gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da yankin gabas ta tsakiya a sabon zamanin da muke ciki.

Zuwa yanzu, bangarorin 2, wato kasar Sin da kasashen yankin gabas ta tsakiya, suna kokarin gudanar da shirin raya "Zirin tattalin arziki na hanyar siliki, da hanyar siliki kan teku ta karni na 21", wato "Ziri Daya da Hanya Daya" a takaice, tare da samun ci gaba a hadin gwiwarsu ta fuskar cinikayya, al'adu, gami da harkokin siyasa, da manyan tsare-tsaren bangarorin 2. Bayan da mista Xi Jinping ya zama shugaban kasar Sin a shekarar 2013, ya cigaba da kokarin bunkasa mu'amala da shugabannin kasashen yankin gabas ta tsakiya, don yaukaka huldar dake tsakanin bangarorin 2, gami da sa kaimi ga hadin gwiwar dake gudana tsakaninsu.

A cewar sharhin jaridar People's Daily, a shekarar 2014, shugaba Xi Jinping ya halarci bikin kaddamar da taron ministoci na dandalin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa, inda ya bayyana burin da za a iya cimmawa bisa gudanar da shirin raya "Ziri Daya da Hanya Daya", don tallafawa kokarin kaddamar da shirin. Daga bisani, cikin tsawon fiye da shekaru 2 da suka biyo baya, yayin da shugaban kasar Sin yake mu'amala da shugabannin kasashen Masar, Iraki, hadaddiyar daular Larabawa ta UAE, da Turkiya, da Jordan, sun mai da hankali sosai kan shirin raya "Ziri Daya da Hanya Daya", wanda ya kasance wani muhimmin bangare cikin hadin gwiwar da ake yi. A sa'i daya kuma, wasu kafofin yada labaru da masana na yankin gabas ta tsakiya na ganin cewa, kasar Sin tana da fasahohi masu daraja a fannin raya tattalin arziki da gina kasa, wadanda za a raba wa kasashen duniya, don haka kamata ya yi, kasashen yankin gabas ta tsakiya sun dora muhimmanci kan kokarin hadin kansu da kasar Sin, musamman ma a fannin tattalin arziki da cinikayya.

Sharhin ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen dake yankin gabas ta tsakiya sun dade suna kokarin tallafawa juna, a kokarinsu na kare mutuncin al'umma, da mulkin kai, da neman raya tattalin arziki da zaman al'umma, haka kuma suna koyon fasahohin junansu a fanin harkokin al'adu. A nata bangare, kasar Sin ba ta tsaya kan hadin gwiwa da kasashen yankin gabas ta tsakiya a fannin tattalin arziki kawai ba, har ma tana daukar matakai don taimakawa daidaita matsalolin dake fuskantar yankin ta fuskar siyasa, da harkar tsaro. Bisa matsayinta na daya daga cikin kasashe masu kujerun naki a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin tana nacewa ga manufarta ta taimakawa daidaita batutuwan da suka shafi yankin gabas ta tsakiya karkashin tsare-tsaren MDD. Abubuwan da kasar Sin take mai da hankali a kai su ne gaskiya da adalci, da bukatun bangarorin dake rikici da juna, don neman samun daidaito tsakaninsu. Idan an waiwayi ci gaban da aka samu bisa matakan da kasar Sin ta dauka, za a gano cewa manufar Sin ta dace da ra'ayin da ya gama gari a duniyarmu, wato neman samun zaman lafiya da ci gaba, da kokarin hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna.

A cewar sharhin, a zamanin yanzu, kasar ta Sin ta fi lura da daukacin kasashen duniya, da kokarin kirkiro sabbin fasahohi don neman ci gaba, musamman ma a lokacin da take kula da harkokin hulda da sauran kasashe. Kasar tana kuma daukar hakikanan matakai don kulla huldar dake amfani ga bangarori daban daban, da sa kaimi ga gyare-gyaren da ake gudanarwa kan tsarin kulawa da harkokin kasa da kasa.

Wannan ziyara da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke yi ta kansance ziyararsa ta farko a bana, don haka ana fatan zai kammala ziyarar cikin nasara, tare da taimakawa kokarin kasar Sin na bunkasa hulda da kasashe daban daban. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China