in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai kai ziyara yankin Gabas na tsakiya
2016-01-18 20:16:40 cri

Bisa gayyatar da sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na kasar Saudiyya da shugaba Abdelfattah al Sisi na kasar Masar, da shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran suka yi masa, shugaban kasar Sin zai kai ziyarar aiki ga wadannan kasashe uku daga gobe, ranar 19 zuwa ranar 23 ga watan. Shugaban kasar Sin ya zabi wadannan kasashe uku na yankin Gabas na Tsakiya, inda ake cikin hali mai sarkakiya sosai da su zama zangon farko a cikin ziyarce-ziyarcen da zai yi a shekarar 2016, wannan ya jawo hankulan duniya sosai. Sakamakon haka, wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Litinin a nan birnin Beijing cewa, ziyarar da shugaba Xi zai kai wadannan kasashen uku za ta zurfafa dangantakar dake tsakanin kasar Sin da su, kuma za ta kawo muhimmin tasiri ga yankin. A yayin ziyararsa, shugaba Xi zai yi musayar ra'ayoyinsa da takwaransa na wadannan kasashe uku kan wasu muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya domin kokarin kawo zaman lafiya a yankin, har ma a duk duniya.

A wani taron manema labaru da aka shirya a yau, Litinin, Mr. Zhang Ming, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, ziyarar aiki da shugaba Xi zai kai wa kasashen Saudiyya da Masar da kuma Iran ziyara ce da shugaban kasar Sin zai sake kawo wa wadannan kasashe uku tun bayan wadanda ya kai a shekaru 7 da na 12 da na 14 bi da bi. A yayin wannan ziyara, shugabannin za su tsara shirin bunkasa fannoni da dangantakar dake tsakaninsu da kasar Sin a nan gaba. An labarta cewa, a yayin da yake kai ziyara a kasar Saudiyya, kasashen Sin da Saudiyya za su fitar da wata sanarwa cikin hadin gwiwa game da yadda za a bunkasa dangantakar abokantaka daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare. Sannan, a yayin da yake ziyarar kasar Masar, shugaba Xi zai halarci kaddamar da yanki na biyu na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen Sin da Masar, da bikin taya murnar cika shekaru 60 da kafa dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, da bikin kaddamar da shirye-shiryen al'adu na shekarar 2016 tsakanin kasashen Sin da Masar.

A karshen makon da ya gabata, an fara aiwatar da yarjejeniyar nukiliya ta Iran. Sakamakon haka, kasashen duniya sun fara soke takunkumin da suka sanya wa kasar Iran. Game da wannan batu, Mr. Zhang Ming ya bayyana cewa, "Kasashen Sin da Iran na da damar bunkasa huldar da ke tsakaninsu, don haka, Sin za ta yi kokarin hada kai tare da Iran, ta yadda ziyarar za ta kai ga ta bude wani sabon babi na huldar da ke tsakanin sassan biyu."

Yankin gabas ta tsakiya wata muhimmiyar mahada ce ga shirin nan na "ziri daya hanya daya" da kasar Sin ta bullo da shi, Mr. Zhang Ming ya ce, wannan shawara ta samu karbuwa daga kasashen da ke yankin, don haka, ta yaya za a tabbatar da shawarar ta jawo hankalin sassa daban daban. Don haka, ana fatan a yayin wannan ziyara za a cimma wasu nasarori a fannonin makamashi da ababen more rayuwa da saukaka harkokin ciniki da zuba jari da kuma makamashin nukiliya da fasahohin sararin samaniya da sabbin makamashi da sauransu. Ban da haka, ana fatan Sin da kasashen ukun za su cimma daidaito a fannonin ilmi da kimiyya da kuma al'adu. Yankin gabas ta tsakiya ta hada nahiyoyin Turai da Asiya da kuma Afirka, haka kuma tekun Atlantic da na Indiya sun hade da yankin, Wannan ya sa yankin yake da muhimmancin gaske. Zhang Ming ya kara da cewa, a lokacin da ya ke birnin Alkahira, shugaba Xi Jinping zai gabatar da jawabi ga kasashen gabas ta tsakiya da na Larabawa, inda zai bayyana manufofin kasar Sin a kan tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, tare kuma da ba da shawarwari a kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da yankin gabas ta tsakiya. "Gaskiya yanayin siyasar Gabas ta Tsakiya na da tasiri ga kasashen duniya, don haka idan har babu zaman lafiya a yankin, hakika ba za a samu zaman lafiya a duniya baki daya ba. Dangane da haka, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya sun samu hanyoyin da za su dace da bunkasuwarsu, haka kuma, kasar Sin tana yin kira ga gamayyar kasa da kasa da su taimakawa kasashen wajen raya harkokin tattalin arzikinsu. A sa'i daya kuma, kasar Sin na fatan za a tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, inda ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su yi kokarin ganin an warware sabani da matsalolin da yankin ke fuskanta ta hanyar yin shawarwari, bisa kundin tsarin MDD da kuma ka'idojin dangantakar kasa da kasa da dai sauransu."

Kaza lika, da yake tsokaci kan matsalar diflomasiyya da ta auku kwanan baya tsakanin kasar Saudiya da Iran, Zang Ming ya bayyana cewa, ana fatan kasashen da abin ya shafa za su kai zuciya nesa, kana su yi kokarin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari. Ya ce, "Kasar Sin na mai da hankali sosai kan yanayin da ake ciki a yankin, tana kuma damuwa domin mai yiyuwa ne wasu al'amura za su tsananta sabanin da ke kasancewa a yankin. Sinawa su kan ce, hadin gwiwa ya kan haifar da alheri, muna fata kasashen yankin za su kai zuciya nesa, sannan su yi kokarin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, kana su hada kai wajen ganin an samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, sabo da lamarin zai dace da moriyar kasashen dake yankin, har ma ga gamayyar kasa da kasa baki daya, ko shakka babu, ciki har da kasar Sin." (Sanusi Chen, Lubabatu Lei, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China