in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kuwait ta sanar da janye jakadanta daga Iran
2016-01-05 20:50:37 cri

A yau ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Kuwait ta bukaci jakadanta dake kasar Iran da ya koma gida.

Kamfanin dillancin labaru na Kuwait ya labarta cewa, wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Kuwait ya sanar da cewa, a yau da safe ne Kuwait ta kirawo jakadanta daga Iran. Jami'in ya kara da cewa, Kuwait ta dauki wannan mataki ne domin nuna rashin amincewa da matakin da Iraniyawa masu zanga-zanga suka dauka na kona ofishin jakadancin kasar Saudiya a Iran. A cewar Kuwait, hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China