in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada sabon kwamandan UNAMID a Darfur
2015-12-15 10:11:38 cri

Magatakardar MDD Ban Ki-moon da shugabar kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Madam Nkosazana Dlamini-Zuma a ranar Litinin din nan suka amince da nadin sabon kwamandan rundunar tsaron ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD da AU a Darfur.

Laftanar Kanar Frank Mushyo Kamanzi daga Rwanda ne aka bayyana a matsayin kwamnadan rundunar ayyukan hadin gwiwwa na wanzar da zaman lafiya ta MDD da AU wato UNAMID, in ji kakakin majalissar da yake bayani ga manema labarai.

Laftanar Kanar Kamanzi zai gaji Laftanar Janar Paul Ignace Mella na kasar Tanzaniya wanda zai kammala wa'adin aikin shi a ranar 31 ga watan nan na Disamba, kakakin ya ce, magatakardar MDD Ban Ki-moon ya gode wa Laftanar Janar Mella bisa ga sadaukar da kai da ya yi wajen gudanar da aikin da aka dora mashi a lokacin wa'adin shi.

Laftanar Janar Kamanzi ya cika kusan shekaru 27 yana aiwatar da aikin soja, kuma yana kwarewar aikin sosai. Kafin wannan nadawa, shi ne babban hafsan soji a rundunar tsaron Rwanda tun daga shekara ta 2012. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China