in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron shugabannin FOCAC karo na biyu zai inganta dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka
2015-12-01 14:43:11 cri

Za a bude taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka (FOCAC) a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a ran 2 ga watan Disamba na bana, inda za a kira taron ministoci karo na shida da kuma taron shugabanni karo na biyu bi da bi a yayin taron, kana wannan shi ne karo na farko da za a gudanar da taron a nahiyar Afirka.

Sassa daban daban daga Afirka na mai da hankali sosai kan taron din da za a kira, sabo da manyan sakamakon da aka samu bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka cikin shekaru 15 da suka gabata, haka kuma, tasirin da kasar Sin take yi a kasashen Afirka na ci gaba karuwa tun kafuwar FOCAC, shi ya sa, a ganinsu, wannan taro na dauke da muhimmiyar ma'ana dangane da ci gaban hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka.

Ga kuma rahoton da Maman Ada ta haha mana kan wannan batu:

Masaniya a fannin harkokin kasa da kasa ta jami'ar Zimbabwe Heather Chingono na ganin cewa, taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka na wannan karo zai kasance wani muhimmin taro cikin tarihin hadin gwiwar Sin da Afirka, kuma bangarorin biyu za su iya yin amfani da wannan dama wajen ciyar da bunkasuwar dangantaka dake tsakaninsu gaba. Sa'an nan kuma, bisa wannan tsari na FOCAC, Sin da Afirka za su iya dukufa wajen cimma moriyar juna cikin hadin gwiwa, da kuma kara yin mu'amala tsakaninsu kan fasahohin neman bunkasuwa. Ta ce, "a farkon taron FOCAC, an mai da hankali kan tattauna yadda za a iya kyautata yanayin tattalin arziki na al'ummomin Sin da Afirka, wadanda adadinsu ya kai rabin adadin mutanen duniya gaba daya, sa'an nan kuma, gwamnatocin kasashen Sin da Afirka sun fara nuna sha'awarsu dangane da raya ababen more rayuwar jama'a, masana'antu da kuma samar da guraben aikin yi ga jama'arsu. Sabo da dukkanmu muna cikin kasashe masu tasowa, shi ya sa, akwai batutuwa da dama da muke iya yin mu'amala a tsakaninmu."

Bugu da kari, ta ce, ko da kasashen Afirka da Sin, dukkansu su kasashe ne masu tasowa, amma, cikin shekaru fiye da 30 da suka gabata, kasar Sin ta samu saurin bunkasuwa sosai a fannin tattalin arziki, tare da samun sakamako masu kyau da dama wadanda suka janyo hankulan kasa da kasa sosai, shi ya sa, ya kamata kasashen Afirka su yi koyi da fasahohin kasar Sin.

Ya kuma kara da cewa, "bai kamata kasashen Afirka su yi koyi da fasahohin kasar Sin daidai da yadda take gudanar da su a kasarta ba, amma, kasashen Afirka muna iya yin koyi daga wajenta a wasu fannonin dake dacewa da halin bunkasuwar kasashenmu na Afirka, ta yadda za a iya raya kasashenmu yadda ya kamata."

Kaza lika, kasar Sin tana kuma taimaka wa kasashen Afirka wajen neman bunkasuwa, yayin dake kokarin raya kanta, musamman ma a fannin taimaka wa kasashen Afirka wajen raya ababen more rayuwar jama'a.

Ya zuwa watan Yuni na shekarar 2015, gaba daya layin dogon da kasar Sin ta gina ko take ginawa a kasashen Afirka ya wuce kilomita 3800, yayin da hanyoyin mota kilomita 4334. Dangane da wannan batu, Brian Mudumi, shugaban taron dandalin tattaunawar matasan Sin da Zimbabwe na ganin cewa, "idan ka duba tsarin layin dogon kasashen Afirka, za ka iya gano cewa, kasar Sin ce take ba da taimako wajen raya wannan tsari, sa'an nan, idan ka duba tsarin wutar lantarkin kasashen Afirka, kamar tashar samar da wutar lantarki da karfin ruwa ta Kariba dake kan iyakar dake tsakanin Zimbabwe da Zambia, za a kuma gane cewa, Sinawa ne suka ba da taimako wajen ginawar tashar. Taron dandalin (FOCAC) yana karfafa dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, yayin da habaka dangantakar zuwa wani sabon matsayi."

Har wa yau, Peter Cagniva wanda ya zo daga jami'ar Nairobi yana ganin cewa, a halin yanzu, kasar Sin tana kasance babbar abokiyar ciniki ta kasar Kenya, a maimakon kasashen Turai ko Amurka. Kasar Sin ta zuba jari da yawa kan bunkasa ababen more rayuwar jama'a a kasar Kenya, wanda ya ba da taimako mai muhimmanci kan raya kasar ta Kenya, ko shakka babu, kasar Sin tana taimaka wa kasar kan kasancewa daya daga cikin kasashen Afirka uku dake fin samun saurin bunkasuwa a duk duniya na halin yanzu.

Tun lokacin da kasar Sin ta shiga Afrika, Sin ta karfafa dangantakar tsakaninta da kasashen Afirka, saurin bunkasuwar kasashen Afirka ya kai kashi biyar bisa dari, lamarin da ya sa, Mr. Cagniva na sa ran gudanarwar taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka na wannan karo sosai, ya ce, "ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ga kasar Afirka ta Kudu zai ba da taimako wajen habaka dangantakar dake tsakanin Sin da Kenya, har ma da dukkanin kasashen Afirka baki daya, muna son yin amfani da wannan dama wajen raya masana'antun Kenya, tare da kara shigar da fasahohin zamani daga masanan kasar Sin."

Kasar Sin da kasashen Afirka na iya habaka hadin gwiwar dake tsakninsu cikin sauki sabo da suna bukatar juna yayin da suke taimakawa juna wajen neman bunkasuwar tattalin arziki da kuma cimma moriyar juna. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China