in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta gamsu da yadda zaben shugaban Burkina Faso ya gudana lami lafiya
2015-12-01 10:22:09 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya fada a ranar Litinin din nan cewar, ya gamsu da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin a Burkina Faso a ranar Lahadin da ta gabata cikin kwanciyar hankali.

Ban, ya taya al'ummar kasar Burkina Faso murna, bisa yadda suka jajurce wajen tabbatar da kafa tsarin mulki na demokaradiyya a kasarsu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun mista Ban ya fitar, ya jinjinawa al'ummmar kasar, musamman mata sakamakon yadda suka fito don kada kuri'unsu a zaben.

A yayin da jama'ar kasar Burkina Faso ke dakon sakamakon zaben, Ban, ya bukaci dukkan shugabannin siyasa da masu ruwa da da tsaki a kasar, da su dauki matakan tabbatar da zaman lafiya a kasar, kamar yadda aka yi a ranar zaben.

Haka zalika, ya bukaci jam'iyyun siyasar kasar da su bi hanyoyin da shari'a ta tanada wajen warware duk wata takaddama da ka iya tasowa a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China