151130-Dr-Sheriff-Ghali-Ibrahim-malami-ne-dake-koyarwa-a-fannin-kimiyyar-siyasa-da-alaka-ta-kasa-da-kasa-a-jamiar-Abuja-Bilkisu.m4a
|
Tun daga shekarar da ta wuce dai, sau da yawa kasashen Afirka suka bayyana fatansu na kara matsayin wannan taro daga taron ministoci zuwa na koli. Saboda haka, an biyan bukatun bangaren Afirka, taron din na karfafa hadin kai irin na samun moriyar juna da nasara tare a tsakanin Sin da kasashen Afirka, da kara imanin kasashen Afirka da kasa da kasa kan bunkasuwar nahiyar Afirka, kana zai sanya kasashen duniya su kara mayar da hankali da zuba jari kan Afirka.
Game da wannan babban taron dai sashenmu na Hausa na CRI mun shirya jerin shirye-shirye, inda muka zanta da wasu jami'ai, masana na Sin da Afirka. A yau ne za mu kawo muku na farko daga cikinsu, inda wakilinmu dake birnin Abuja na kasar Najeriya Murtala ya zanta da Dr. Sheriff Ghali Ibrahim, malami ne dake koyarwa a fannin kimiyyar siyasa da alaka ta kasa da kasa a jami'ar Abuja. To, yanzu sai ku biyo mu cikin zantawar tasu.