in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori daban daban na kasar Zimbabwe na zura ido kan ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar
2015-11-30 14:43:13 cri

Daga ranar 1 zuwa 2 ga wata mai zuwa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasar Zimbabwe, wannan ne karo na biyu da wani shugaban Sin zai kai ziyara a kasar cikin shekaru kusan 20 da suka wuce. Bangarori daban daban na kasar Zimbabwe suna marhabin da wannan ziyara, suna kuma fatan ziyarar mai muhimmanci za ta kasance wata gadar da za ta hada kasashen biyu.

Yanzu ga Karin bayanin da abokiyar aikinmu Bilkisu za ta kara mana.

Shugaban dandalin tattaunawa na matasan kasashen Zimbabwe da Sin Brian Mudumi yana mai cewa, ziyarar da shugaba Xi zai kai kasar za ta karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. 

"An taba gano kudin Sin a lokacin da ake wasu gine-ginen tarihi a kasar Zimbabwe, wannan ya nuna cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na da dogon tarihi. A baya kasashen biyu sun yi kokarin gudanar da yakin 'yantar da jama'a, tun bayan Zimbabwe ta samu 'yancin kai kuma, dangantakar dake tsakaninsu na kara samun bunkasuwa. Ziyarar da shugaba Xi zai yi za ta kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Muna maraba sosai da ziyararsa, muna kaunar sa."

Tsohon jakadan kasar Zimbabwe dake kasar Sin, kuma ministan kula da harkokin sojojin da suka yi ritaya Christopher Mutsvangwa ya ce, kasarsa da kasar Sin tsoffin abokan juna ne, tsohon shugaban kasar Sin Jiang Zemin ya taba kai ziyara a Zimbabwe a shekarar 1996. Kasar Zimbabwe ta dade tana fuskantar matsalar tattalin arziki, saboda haka tana fatan fita daga wannan kangi bisa taimakon kasar Sin.

"Yanzu kasar Sin ta kasance kasa ta biyu cikin kasashen da tattalin arzikinsu ke samun saurin bunkasuwar tattalin arziki, tana kuma taka muhimmiyar rawa wajen farfado da tattalin arzikin kasashen Afirka. Bunkasuwar tattalin arzikin Afirka na da alaka kai tsaye da shigar da kasar Sin cikin dandalin tattalin arzikin duniya. Muna ganin cewa, wannan wata dama ce mai kyau wajen sake dawo da dandalin tattalin arzikin duniya. Muna fatan kasar Sin za ta taimaka mana domin cimma wannan burin."

A nata bangaren, masaniya a fannin nazarin batutuwan duniya ta jami'ar Zimbabwe Heather Chingono tana ganin cewa, ziyarar da shugaba Xi Jinping zai yi na da ma'ana sosai ga Zimbabwe.

"Mun ganin cewa, kasar Zimbabwe za ta yi farin ciki da ziyarar wannan shugaban da ya fi muhimmanci a duniya, wannan ziyara na da ma'ana sosai ga kasarmu. Kana wata dama ce mai kyau a gare mu, muna kuma fatan nuna wa shugaban irin ayyukan hadin kai da muke fatan gudanarwa. A matsayinsa na jagorar kasar Sin, shugaba Xi zai kalli hakikanin yanayin da Zimbabwe ke ciki, ta yadda zai fahimci yiwuwar zuba jari a kasar Zimbabwe."

Shugabar cibiyar nazarin dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka da ke kudancin Afirka Phyllis Johnson ita ma tana da ra'ayin cewa, ziyarar da shugaba Xi zai yi a Zimbabwe za ta kai ga daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

"Shugaba Xi Jinping zai samu tarba sosai a kasar Zimbabwe, mutane da yawa za su yi masa maraba. Wannan wata ziyara ce a tsakanin kasashe 'yan uwa, kuma ta sada zumunta sosai. Amma, ba ziyarar yau da kullum ba ce, za a samu hakikanin sakamako a wasu fannoni. A yayin ziyarar, shugaba Xi da shugaba Mugabe za su tattauna kan wasu batutuwa, za kuma su sa hannu kan wasu yarjejeniyoyi, wadanda za su taimaka wa kasar Zimbabwe matuka, ta la'akari da yadda take karkashin takunkumin da kasashen yammacin duniya suka kakaba mata. Yanzu kasar Zimbabwe ta shirya sosai, domin maraba da zuwan shugaba Xi, kuma tana shirin daga matsayin dangantakar dake tsakanin ta da Sin zuwa wani sabon matsayi. Lallai muna zura ido sosai kan wannan ziyara."
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China