in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa ne harbo jirgin saman Rasha da Turkiya ta yi ya lahanta dangantakar kasashen biyu
2015-11-25 14:17:15 cri

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu dake Turkiya, ya ce wasu jiragen saman yaki guda biyu na kasar, sun harbo wani jirgin saman yaki na kasar Rasha a kan iyakar kasar da Syria, bayan sun yi masa gargadi sau da yawa. A nata bangaren kasar Rasha ta ce an harbo jirgin saman yakin nata ne a sararin saman kasar Syria kusa da kan iyakar Turkiya.

Kafofin watsa labarai da dama sun yi hasashen cewa mai yiwuwa lamarin ya haddasa tabarbarewar dangantaka tsakanin kasashen Turkiya da Rasha, a sa'i guda kuma zai kara tsanantar yanayin da Syria ke ciki.

Bayan faruwar lamarin dai, ofishin firaministan kasar Turkiya ya bayyana cewa, zai ba da rahoto game da lamarin ga kungiyar tsaro ta NATO da kuma MDD. A jiya Talata ne ma'aikatar harkokin wajen kasar ta gana da jakadun kasashe zaunannun mambobin kwamitin sulhun MDD, wato kasashen Sin, da Amurka, da Burtaniya, da Faransa da kuma Rasha dake kasar ta. A daya bangaren kuma, a dai wannan rana shugaban kasar ta Turkiya ya kira wani taron tsaro na gaggawa.

Kaza lika ita ma kungiyar tsaro ta NATO ta kira na ta taron gaggawa domin tattauna wannan lamari na harbo jirgin saman yakin Rasha.

Har wa yau shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin ya ce wancan jirgin saman yaki na aiki ne na murkushe dakarun dake yankin arewacin Lattakia na kasar Syria, bai kuma haifar da wata barazana ko kadan ba ga kasar Turkiya. Ya kara da cewa, kullum kasar Rasha na daukar Turkiya a matsayin aminiya, don haka bai san dalilin da ya sa ta harbo jirgin saman yaki na Rasha ba. Baya ga haka, Putin ya ce kasarsa ba za ta yafe irin wannan babban laifi ba, kuma martanin sa zai haifar da tasiri mai tsanani ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A kwanan baya, an samu takun-saka tsakanin kasashen biyu a yankin dake kan iyakar Turkiya da Syria, inda kasar Turkiya ta taba sanar da cewa, sau da yawa jiragen saman yakin Rasha sun keta sararin saman ta, bayan sun kai hari ta sama kan mayakan kungiyar IS dake kasar Syria tun daga ranar 30 ga watan Satumba, yayin da kasar Rasha ta soma hada kai da sojojin kasar Syria wajen murkushe kungiyar.

Firaministan kasar Turkiya Ahmet Davutoglu ya taba yiwa Rasha kashedin kada ta kara keta ikon mallakar sararin saman kasar sa, yana mai cewa aikata hakan zai sa kasar sa daukar matakai. Bayan faruwar wannan lamari, firaministan ya kara jaddada cewa Turkiya za ta dauki ko wane irin matakai domin kiyaye tsaro da zaman lafiya a yankunan ta, da kuma yankunan dake kewayen ta.

Kasashen Turkiya da Rasha suna da moriyar bai daya a yankin tekun Black Sea, kuma suna da sabani a kan batun tekun. A 'yan shekarun da suka wuce, kasar Turkiya na mayar da hankali sosai kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da Rasha, kana hadin kai a tsakaninsu a fannonin tattalin arziki, da cinikayya, da makamashi na samun ci gaba.

Bugu da kari cikin tsahon lokaci kasar Turkiya na dogaro kan Rasha wajen shigo da makamashi, a sa'i daya ta kasance daya daga cikin muhimman kasashen dake samar da kayayyakin aikin gona na kasar ta ga Rasha. Sai dai a matsayin ta na kasa mamba a kungiyar NATO, tana goyon bayan dakarun adawar kasar Syria, tana kuma adawa da mulkin Bashar al-Assad, wanda hakan ya haifar da sabani tsakanin ta da Rasha.

Manazarta na ganin cewa, wannan lamari na harbo jirgin saman yaki, mai yiwuwa ya hargitsa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ana kuma ganin cewa hakan, zai haifar da tasiri ga dangantakarsu cikin gajeren lokaci.

Ban da haka kuma, lamarin na iya kara lalata yanayin da yankin Syria ke ciki. Yanzu haka dai ana zura ido don ganin matakan da kasashen biyu za su dauka. Wato ko za su nuna juriya, ko kuma za su kara rura wutar rikici a tsakaninsu. Kana za a ga irin tasirin da hakan zai yi ga kasar Rasha, da kungiyar NATO game da batun Syria da ma ayyukan murkushe kungiyar IS.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China