in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nada sabon shugaban UNSOM a Somaliya
2015-11-24 10:09:43 cri

Magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Litinin din nan ya sanar da nadin Micheal Keating, 'dan kasar Birtaniya a matsayin sabon wakilin musamman nasa a Somaliya, kuma shugaban ofishin ayyukan ba da tallafi a kasar wato UNSOM.

Micheal Keating zai maye gurbin Nicholas Kay wanda zai kamala wa'adin shi a karshen shekarar nan da muke ciki.

Magatakardar na MDD ya mika godiyar shi ga Mr Kay bisa ga kwazo da sadaukar da kai da gaggarumin gudunmuwar da ya bayar a lokacin wa'adin aikin shi a UNSOM cikin shekaru 2 da rabi da suka gabata, lokacin da ya kasance mai tsanani a yanayin siyasar kasar, in ji kakakin majalissar Stephane Dujarric a ganawar da ya yi da manema labarai.

Ya yi bayani cewa, Mr Keating ya kware wajen aikin siyasa da gina kasa, har ma da aikin jin kai a Afghanistan, Gabas ta Tsakiya da Afrika.

A matsayin shi na mataimakin darekta na cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta fadar Chatham tun daga shekara ta 2012, ya kuma yi aiki a matsayin babban mai ba da shawara ga manzon musamman na magatakardar MDD a Syria. Kuma shi ne mataimakin wakili na musamman na magatakardar MDD, da kuma mai yin sulhuntawa kan aikin jin kai na MDD a Afghanistan daga shekara ta 2010 zuwa 2012.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China