in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin Sin da Afrika mai zuwa zai karfafa dangantaka tsakanin bangarorin biyu
2015-11-19 10:53:02 cri
Wani jami'in gwamntin Afrika ta Kudu a ranar Laraba ya bayyana cewa, dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da Afrika (FCSA) da za a shirya a ranakun 4 da 5 ga watan Disamba a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu, na da muhimmancin gaske domin zai bude kofa wajen kara bunkasa dangantaka tsakanin bangarorin biyu.

Jakada Ghulam Asmal, na ma'aikatar harkokin wajen Afrika ta Kudu, ya bayyana cewa, wannan dandali zai samar da sabbin dabarun karfafa dangantaka. Kuma zai kasance bisa taken "Sin da Afrika tafiya tare bisa dangantakar moriyar juna domin wata bunkasuwa ta hadin gwiwa".

Muna fatan za'a sanar a da wani babban matakin dangantakar mai alfanu, kuma taron zai kawo wani karin yunkuri ga tsarin cigaban Afrika, in ji mista Asmal.

Za mu kara tunanin yin musanyar kwararru da wani taimakon kasar Sin ga nahiyar Afrika domin tallafawa cigaban masana'antunta, in ji jami'in.

Kasar Sin na tuntubar kasashen Afrika 41 game da wani shirin aiki da za'a gabatar a wannan dandali, a cewar mista Asmal.

Jami'an diplomasiyyar Afrika sun gudanar da taruka tare da kasar Sin da suka shafi sanarwar taron FOCAC da sauran takardun da za a sanya ma hannu a yayin wannan dandali. Wakilan gwamnatoci da kamfanoni za su yi ganawa domin tattauna batutuwan dake janyo hankalinsu, da suka shafi sassaunci rance, bunkasa zuba jari a fannin kimiyya da fasaha, yaki da zaman kashe wando musammun ma na matasa, da kuma kawar da talauci, in ji mista Asmal. Tare da kara cewa, Afrika na daukar wannan dandali bisa wani matsayi na girmama juna, ba wai irin taron masu bada lamuni ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China