in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tunkarar hadin gwiwwar moriyar juna don ci gaba mai dorewa
2015-11-03 10:22:41 cri
Xi JinPing, shugaban kasar Sin

a cibiyar MDD dake birnin New York

26 Satumban 2015

'Yan uwana shugabannin taro,

Masu girma abokan aiki,

Na yi matukar farin cikin halartar wannan taro na yau. Ganin MDD na cika shekaru 70 da kafuwarta, wannan yana da matukar muhimmanci kuma taron ya samar da lokacin da Shugabannin duniya za su hadu waje daya a New York don tattauna ci gaba dake tafe.

Ci gaba yana dauke da fata da ainihin rayuwar kowane al'umma na dukkan kasashe. Yana bayyanar da darajarsu da 'yancinsu. A cikin irin haka ne aka tsara muradan karni na shekaru 15 da suka gabata a kokarin da ake na inganta rayuwar miliyoyin al'ummomi.

A cikin shekarun da suka ratsa tsakani mun ga kara ci gaba a duk fadin duniya da kuma matsanancin tabarbarewar tattalin arziki ga yadda dukkanin bangarorin suka shafi kasashe masu tasowa da kuma tangal tangal tsakanin arewa da kudu. Baya ga murnan cewa fiye da mutane biliyan daya da miliyan daya sun tsira daga cikin kangin talauci, hakan bai hana mu damuwa ba matuka na cewar fiye da mutane miliyan 800 har yanzu sun kwana ba tare da samun abin da suka saka a baki ba.

A matakin na duniya, zaman lafiya da ci gaba ya kasance babban jigo na kowane lokaci. Ta yadda za'a tunkari kalubaloli da dama da muke fuskanta da suka hada da matsalar 'yan gudun hijira da yanzu haka ake fama da ita a nahiyar Turai, babu wata mafita da ta wuce a nemi zaman lafiya da ci gaba. Yadda aka fuskanci irin wadannan kalubaloli masu sarkakkiya da wahaloli, dole ne mu rike ci gaba a matsayin babban madafarmu, domin dole sai ta ci gaba ne za mu iya warware ainihin matsalolin da muke fuskanta, kare 'yancin al'ummarmu da kuma tunkarar fata na gari da al'ummar tamu ke da shi na rayuwa mai kyau a nan gaba.

'Yan uwana, shugabannin taro,

Masu girma abokan aiki,

Sakamakon ayyukan ci gaba bayan shekara ta 2015 da wannan taron ya amince da shi ya fitar da sabon jadawali na ci gaban duniya tare da samar da sabon daman a hadin gwiwwar kasa da kasa. Ya kamata mu dauki wannan a wani sabon mafari, mu fitar da shirin mai daidaito, a bayyane, a kowane zagaye tare da zummar kirkiro da ayyukan ci gaba da kuma himma wajen cimma matsaya daya a dukkan kasashe.

----MUNA BUKATAR DAIDAITON CI GABA. Dukkan kasashe ya kamata su samu 'yancin daidaito a matsayinsu na masu shiga a dama da su wajen ba da gudunmuwa, su kuma amfana daga ayyukan ci gaba na duniya. Wannan ba zai zama wani dama ba kawai ga mutum daya ko wassu daidaikun kasashe ba, kuma sauran kasashe masu yawa su kasa amfana daga ciki. Kasashe za su samu banbanci saboda iyawar karfinsu na ci gaba da kokarin da suka yi wajen cimma muradansu, amma suna dauke da manufa daya kuma kamar kowa, idan aka banbanta, a matakin karfinsu. Yana da muhimmanci a inganta jagorancin tattalin arzikin duniya, a kara wakilcinsu, kuma da muryar kasashe masu tasowa sannan a ba dukkan kasashen dama daidai wa daida su shiga a dama da su a harkokin fada a ji a duniya.

----MUNA BUKATAR TABBATAR DA CI GABA A BAYYANE, MU ISAR DA MORIYA GA DUKKAN BANGARORI. Da natsuwar da aka samu na tafiyar tattalin arziki a duniya, dukkan kasashe ya kamata su bar kofofinsu a bude su kuma bar dalilan samarwa ya shiga a tsanaki kuma cikin lumana a duk fadin duniya. Yana da muhimmanci ga kasashe su rike tsarin ciniki na kowane fanni, su gina tattalin arziki a fili sannan su rarraba ribar ta hanyar tattaunawar fahimtar juna da hadin gwiwwa. Ya kamata mu mutunta ra'ayin juna na hanyar ci gaba, mu yi koyi daga sakamakon junanmu, mu kawo wadannan hanyoyi daban daban waje daya a matakin nasara, ta haka za mu amfana daga ci gaban dukkan al'umma.

----MUNA BUKATAR TABBATAR DA CI GABA A KOWANE BANGARE DOMIN TUSHE YA YI KARKO. Ci gaba a karshe shi al'umma ke bukata. Lokacin da ake kokarin yaye talauci da inganta rayuwar al'umma, yana da muhimmanci a gare mu na yin tsayin daka a kan akidar daidaici da hakkin al'umma da kuma tabbatar da cewa kowa yana da 'yanci ga samun dama da riba na ci gaba. Dole a kara kokari wajen daidaita tattalin arziki, al'umma da muhalli sannan a cimma zamantakewa cikin lumana tsakanin dan adam da sauran al'umma, kuma tsakanin dan adam da halittu.

----MUNA BUKATAR TABBATAR DA CI GABAN KIRKIRE KIRKIRE DON FITAR DA BASIRA. Kirkire-kirkire wani abu ne mai mahuimmanci. Matsalolin da kan bullo sakamakon ci gaba za'a iya warware shi ta hanyar kara ci gaba. Dole ne dukkan kasashe su nemi hanyoyin yin kwaskwarima da kirkire-kirire dan a samu kafar fito da basirarsu, gina na'urori masu karfi wajen ci gaba, sannan a habaka himmarsu na yin takarar iya karfinsu.

'Yan uwana shugabannin taro,

Masu girma abokan aiki.

Jadawalin ci gaba na bayan shekara ta 2015 yana dauke da jerin bukatun da ake son isarwa daga kokarin da muke da shi. Ana yawan cewa darajar kowane shiri yana tare ne da yadda aka aiwatar da shi. Don haka na yi kira ga dukkannin kasa da kasa da su rubanya kokarin da suke tare wajen ganin an cimma jadawalin da aka shirya na bayan shekara ta 2015 sannan kuma a yi aiki tukuru na ganin an cimma wannan buri.

----NA DAYA, A HADA KARFI DON CI GABA. Ci gaba, a karshe dai ana nufin aiki ne na kowace kasa ita kadai. Mu Sinawa mu kan ce, "Ka ci bisa girman cikinka kuma ka saka tufafi daidai girman jikinka'', yana da muhimmanci don haka ga kowace kasa ta shirya nata dabarun ci gaban da ya dace da karfinta da yanayinta. Kasa da kasa suna da nauyin a wuyan su na taimakon kasashe masu tasowa wajen inganta karfinsu da kuma ba su goyon baya da taimakon da yaje daidai da bukatunsu.

----NA BIYU, INGANTA YANAYI NA KASA DA KASA DOMIN CI GABA. Zaman lafiya da ci gaba suna tafiya kafada da kafada. Ya kamata kasashe su yi aiki tare don tabbatar da zaman lafiya a duniya, inganta ci gaba tare da zaman lafiya da kuma samar da zaman lafiya ta hanyar ci gaba. Ana bukatar yanayi mai kyau domin ci gaba ya inganta. Hukumomin kudi na duniya don haka suna bukatar su kara azama a kwaskwarima shugabancinsu da kuma cibiyoyi daban daban na ci gaba suna bukatar kara kaimi wajen samar da kayayyakinsu.

----NA UKU, A RIKA BA DA BAYANIN A KAI A KAI NA HADIN GWIWWA DON CI GABA. Kasashen da suka ci gaba ya kamata su cika da kuma tabbatar da aiwatar da alkawuransu a kan lokaci. Al'ummomin kasa da kasa, a lokacin da suke aiwatar da aikinsu a matsayin hadin gwiwwa tsakanin kudu da arewa a matsayin babbar hanya, ya kamata su inganta ayyukansu don kara karfi a hadin kan kudu da kudu, su kuma kara rubanya hadin gwiwwa da karfafa gwiwwa ma hukumomi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki su taka rawar sosai a wadannan hadin gwiwwa.

----NA HUDU, A KARFAFA KAFOFIN GUDANARWA NA CI GABA. Kasashen na bukatar inganta kokarinsu a kananan tsarin tattalin arziki don kauce ma yiwuwar samun akasi da ka iya biyo baya. Hukumomin yankuna ya kamata su gaggauta cudanyarsu da kuma kara masu karfi a dukkan takararsu ta hanyar zakulo karfin yankunansu. Dole ne MDD ta aiwatar da aikinta na shugabanci.

'Yan uwana shugabannin taro,

Masu girma abokan aiki.

A cikin shekaru 30 da ma fiye tun lokacin da kasar Sin ta fara kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje. Kasarmu ta bi tsarin ci gaba mai yanayi da halayyar Sinawa zalla. Wanda aka zaba ta la'akari da yanayin da kasar ke ciki. Ta hanyar nasararmu ta fitar da mutane miliyan 439 daga kangin talauci da kuma ingantaccen ci gaban da muka samu a bangarori kamar ilimi, kiwon lafiya da walwalan mata a zahir, mun cimma muradan karninmu. Ci gaban kasar Sin ba kawai ya inganta rayuwar al'ummar Sinawa sama da biliyan 1.3 ba ne har ma ya ba da babban karfi ga ci gaban duniya.

A fiye da shekaru 60 da suka gabata, kasar Sin ta shiga ayyukan hadin gwiwwar kasa da kasa tukuru. Mun samar da taimako da kayayyakin aiki na ci gaba da ya kai kwatankwacin kudi kusan RMB biliyan 400 ga kasashe 166 da hukumomin kasa da kasa, sannan muka aika da ma'aikatan bada agaji fiye da 600,000, har ma fiye da 700 daga cikinsu sun rasa rayukansu a lokacin aikin samar da ci gaba ga wassu kasashe.

Idan aka hangi gaba, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da daidaito tsakanin 'yancinta da abin da zai amfane ta ta hanyar saka 'yancin kafin irin wadannan abin da take so. Za mu hada hannu da sauran kasashe a kokarin cimma jadawalin bayan shekara ta 2015. Don haka a nan, ina son yin sanarwa kamar haka:

--Kasar Sin za ta kafa asusun tallafi don ayyukan hadin gwiwwa na kudu da kudu, kuma za ta kebe kudin alkawari dalar Amurka biliyan 2 domin taimaka ma kasashe masu tasowa a cikin ayyukansu na jadawalin bayan shekara ta 2015.

--Kasar Sin za ta ci gaba da kara zuba jari a kasashe mafi baya kwarai wajen ci gaba, da nufin cimma dalar Amurka biliyan 12 nan da shekara ta 2030.

--Kasar Sin za ta yafe ruwa da yake kan basukanta tsakanin gwamnatocin kasashe masu tasowa, kasashen da ke fuskantar kunci ci gaba da kananan tsibiran kasashe masu tasowa.

--Kasar Sin za ta kafa cibiyar ci gaba ta samar da ilimi ta kasa da kasa domin karatu a kai da kuma musanya tsakanin kasashe a kan fasahohin da sakamakon da aka samu na cigaba da zai dace da su.

--Kasar Sin za ta shirya wani tattaunawa don kafa yanar gizo ta duniya mai amfani da makamashi don taimaka ma kokarin da ake na cimma karfin kasa da kasa a bukatar samar da yanayi mai tsafta.

Kasar Sin haka kuma a shirye take kuma ta yi niyya na aiki da sauran masu ruwa da tsaki don samar don gaggauta ci gaba wajen aiwatar da shirin "ziri daya hanya daya", don gaggauta fara aikin bankin samar da ababen more rayuwa na yankin Asiya da kuma bankin kungiyar BRICS, haka kuma don ta ba da gudunmuwa ga ci gaban tattalin arziki na kasashe masu tasowa da inganta yanayin rayuwan al'ummarsu.

'Yan uwana shugabannin taro,

Masu girma abokan aiki.

Mu, al'ummar kasar Sin mun yi wannan alkawarin. Na daukaka kokarinmu wajen aiwatar da ayyukan jadawalin bayan shekara ta 2015 a matsayin nauyin da yake kanmu, mu yi aiki tare da sauran kasashen duniya a matsayin daya, kuma mu kara azama a duk ayyukan ci gaban duniya.

Na gode.

(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China