in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta zo da sakon zaman lafiya
2015-11-03 10:21:41 cri
Jawabi ga taron zaman lafiya na MDD

Xi Jinping, shugaban kasar Sin

a cibiyar MDD dake birnin New York

28 ga watan Satumbar 2015

Shugaba Obama,

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon

Ya abokan aiki,

Ina matukar jinjinawa shugaba Obama saboda kiran wannan taro da ya yi.

Sanin kowa ne zaman lafiya abu ne da daukacin al'ummar duniya ke burin samuwarsa. A kuma bisa burin hakan ne aka samar da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD. A yanzu wannan aiki ya zamo ginshikin wanzar da zaman lafiya da lumana, ya kuma samar da kwarin gwiwa ga yankunan da rikice-rikice suke addaba, tare da baiwa al'ummun irin wadannan yankuna kyakkyawan fata na fita daga kangi.

A daidai wannan gaba da muke magana, akwai al'ummu da dama a yankuna daban daban dake fama da yake-yake cikin mawuyacin hali. Wadannan al'ummu na fatan samun zaman lafiya, suna bukatar karin tallafi daga MDD, da kuma gudummawa daga ayyukan wanzar da zaman lafiya. Don gane da hakan ga matsayar kasar Sin.

----Ya zama wajibi a yi biyayya ga daukacin ka'idojin wanzar da zaman lafiya.

Ya zama wajibi a tabbatar da biyayya ga ka'idojin MDD, da kuma manufofin "Hammarskjold" tare da dukkanin kudurorin dake karkashin ayyukan wanzar da zaman lafiya. Kana ya kamata a aiwatar da dokokin kwamitin tsaron MDD baki daya, ta yadda ba za a kyale wata kasa ta zamo shafiffiya da mai ba. Har wa yau, kamata ya yi a ci gaba da gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya tare da kudurce bukatun al'ummun da abun ya shafa a zuci. Kana a tsara, tare da zartas da manufofin kammalar irin wadannan ayyuka cikin lokaci kuma yadda ya kamata.

----Akwai bukatar kara inganta tsarin gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Ya kamata a ci gaba da yi wa ayyukan wanzar da zaman lafiya gyaran fuska, ta yadda za su dace da manufofin diflomasiyya na kariya, da ginin zaman lafiya mai dorewa. A lokaci guda kuma, kamata ya yi a ci gaba da shigar da tsarin shiga tsakani, da martaba dokokin kasashe, da sulhu tsakanin al'ummu, tare da daga matsayin zamantakewar jama'a. Ya dace kwamitin tsaron MDD ya kara azama, wajen sauraron ra'ayoyin sassa masu ruwa da tsaki, da ma ra'ayoyin kasashen dake tallafawa da dakaru. Ya dace a kafa tsarin gudanar da hadin gwiwar ayyukan wanzar da zaman lafiya tsakanin MDD da sauran hukumomin yankunan dake taka rawa a wannan fanni.

----Ya dace a kyautata tsarin bada dauki.

Kara kyautata ayyukan wanzar da zaman lafiya na iya ba da damar cimma nasarori, da ba da cikakken lokaci na kare rayukan jama'a. Sin na maraba da kafuwar sabon tsarin MDD na kar ta kwana game da ayyukan wanzar da zaman lafiya, tare da kira ga sauran kasashe mambobin majalissar da su shiga a dama da su cikin tsari.

----Ya dace a kara fadada tallafin da ake baiwa nahiyar Afirka.

Nahiyar Afirka na matukar bukatar taimakon wanzar da zaman lafiya. Ko shakka babu akwai bukatar kasashen duniya, da MDD su kara yawan tallafin da suke baiwa kasashen Afirka wajen wanzar da zaman lafiya da lumana, ta yadda nahiyar za ta iya magance matsalolin ta gwargwadon bukatar al'ummun ta.

Ya abokan aiki,

A matsayinta na mamba a kwamitin tsaron MDD, Sin ta shafe shekaru 25 tana shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya. Muna cikin manyan masu samar da kudade, da dakaru domin nasarar wadannan ayyuka. Domin tallafawa ci gaba da karfafa wannnan aiki, ina bayyana cewa:

Da farko Sin za ta shiga sabon tsarin MDD na kar ta kwana game da ayyukan wanzar da zaman lafiya. Don haka ne ma muka shirya tsaf domin shigewa gaba, a fagen samar da rundunar 'yan sandan wanzar da zaman lafiya, da ta masu aikin wanzar da zaman lafiya na ko ta kwana mai kunshe da jami'ai 8,000.

Na biyu, Sin za ta ci gaba da baiwa bukatun MDD kulawa, ta hanyar samar da injiniyoyi sojoji, da ma'aikatan sufuri da na lafiya, domin tallafawa ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Na uku, cikin shekaru biyar masu zuwa, Sin za ta horas da jami'an wanzar da zaman lafiya 2,000 daga kasashe daban daban, za kuma ta ba da tallafi wajen samar da horo, da ba da kayayyakin aiki a fannin tone ababen fashewa har karo 10.

Na hudu, cikin shekaru biyar masu zuwa, a karon farko Sin za ta tura jirginta mai saukar ungulu, domin shiga aikin wanzar da zaman lafiya na MDD a nahiyar Afirka.

Na biyar, za a yi amfani da wani sashe na kudaden hadin gwiwar Sin da MDD na ayyukan wanzar da zaman lafiya da ci gaba, domin tallafawa wanzar da zaman lafiya.

Ya abokan aiki,

Sinawa maza da mata su 18 masu kayan sarki sun rasa rayukansu a aikin wanzar da zaman lafiya, yau da shekaru 5 da suka wuce mun yi rashin He Zhihong, 'yar sanda mai aikin wanzar da zaman lafiya a Haiti. Ta bar yaro dan shekaru 4, da iyayenta tsaffi. Ta taba rubuta cewa, "A wannan duniya mai fadi, ko da yake ban wuce dan gashi karami ba, amma duk da haka, ina fatan wannan dan gashi zai dauki sako na zaman lafiya."

Wannan shi ne burinta, kuma shi ne aniyar kasar Sin game da zaman lafiya.

Na gode.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China