in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda za a inganta rayuwar mata da gina duniyar da za ta dace da kowa da kowa
2015-11-03 10:20:13 cri
Xi Jinping shugaban kasar Sin

a yayin taron shugabannin kasashen duniya game da daidaiton jinsi da 'yancin mata a MDD

Ranar 27 ga watan Satumba, 2015

Babban sakataren MDD, Ban Ki-moon

Babbar darekta Phumzile Mlambo-Ngcuka

Abokai,

Maza da mata,

Yayin da ake bikin cika shekaru 70 da kafuwar MDD da bikin cika shekaru 20 da taron mata na duniya da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin, yana da muhimmanci matuka a gare mu mu kira wannan taro na shugabannin kasashen duniya domin sake jadadda kudurinmu na samar da daidaiton jinsi da kuma 'yancin mata kana mu tsara shirye-shirye don samun makoma mai kyau a nan gaba.

Mata wata halitta ce mai daraja, wadanda suke wakiltar wani kaso mai matukar muhimmanci a bangaren jin dadi da kuma ci gaban rayuwar jama'a. Idan har babu mata, to, babu ci gaban bin-Adam ko kuma al'umma baki daya. Gwagwarmayar da ake game da daidaiton jinsi batu ne mai fa'ida. Tarihi ya nuna cewa, muddin mata ba su samu 'yanci da ci gaba ba, to, dan-Adam ma kansa ba zai samu 'yanci da ci gaba ba. Wannan ya sa muka cimma wani zango mai nisan gaske kafin mu cimma nasara game da daidaiton jinsi. Sannan daga lokacin da aka wallafa dokar da ta shafi 'yancin mata sama da shekaru 200 da suka gabata har zuwa lokacin da ake bikin ranar mata ta duniya a ranar 8 ga watan Maris, sannan daga lokacin da aka kafa hukumar kula da matsayin mata ta MDD har zuwa lokacin da aka kaddamar da taron yaki da duk wasu nau'o'in nuna kyama ga mata, duk wani mataki da aka dauka a kokarin da ake na samar da daidaito ga mata ya taka muhimmiyar rawa ga ci gaban wayewar kan bil-Adam.

Taron mata na duniya da aka a yi a Beijing shekaru ashirin (20) da suka gabata, ya amince da sanarwar Beijing, wadda ta zayyana manufofi da kuma matakan da za a dauka kan bunkasa daidaiton jinsi da kuma tabbatar da 'yancin mata. A yau matakan da aka gabatar a taron na Beijing ya haifar da gagarumin canji a duniya baki daya. Yarjejeniyar da kasashe suka cimma game da batun daidaiton jinsi na kara karfafa. An kuma dauki matakai daban-daban kan yadda za a bunkasa ci gaba mata, Sannan rayuwar mata baki dayanta na inganta. A saboda haka, kamata ya yi mata su san irin gagarumar rawar da MDD ta taka na samar musu da hurumi a cikin al'umma.

Godiya ga shekaru da dama da aka kwashe ana fafufukar ganin tabbatar mafarkin da ake a baya ya zama gaskiya: Yanzu haka akwai kasashe 143 da suka sanya batun daidaiton jinsi cikin dokokinsu, matakin da ya taimaka wajen kawar da shingen da ke hana mata shiga a dama da su cikin harkokin siyasa da tattalin arziki, sannan yanzu haka an cimma yarjejeniya a duniya baki daya cewa, kamata ya yi a baiwa mata damar samun ilimi da aikin yi da kuma 'yancin auren wadanda suke so.

Ko da yake har yanzu ana nuna bambanci tsakanin maza da mata a yawancin sassan duniya dangane da cin gajiyar wasu albarkatu. A wasu wuraren har yanzu ba a ci gajiyar hazaka da irin gudummawar da mace za ta iya bayarwa. Yawan mata ya kai sama da miliyan 800 na yawan al'ummar duniya. Sannan su ne ke dandana akubar yake-yake da cututtuka, ayyukan ta'addanci da tashe-tashen hankula. Har zuwa wannan lokaci da muke magana a nan, mata na ci gaba da fuskantar nau'o'in nuna wariya da cin zarafi iri daban-daban.

Wannan ya nuna cewa, har yanzu akwai sauran aiki game da kokarin da ake na samar da daidaiton jinsi. Wajibi ne mu kara daura damara a wannan fafutuka.

Abokai,

Maza da Mata,

Mun cusa batun yadda za a inganta daidaiton jinsi cikin ajandar bunkasa bayan shekarar 2015 da muka amince ba da dadewa ba. Don haka, ya kamata mu sake jaddada kudurin taron Beijing tare da kara daura damara ba tare da bata lokaci ba dangane da bunkasa batun daidaiton jinsi da mata a dukkan harkokin ci gaba.

Da farko, ya kamata mu yi gwagwarmayar nema wa mata 'yanci ta yadda zai dace da jin dadin rayuwa da ci gaban tattalin arziki. Babu wani ci gaban da za a samu idan har babu mata, sannan wajibi ne kowa ya amfana da ci gaban da aka samu. Kamata ya yi mu bullo da dabarun ci gaban da kowa zai taka rawa ta hanyar la'akari da yanayin kasa, bambancin jinsi da muhimman bukatun mata da manufofin da za su kare 'yancin mata wajen cin gajiyar ci gaban da aka samu. Bugu da kari, kamata ya yi a yi wa manufofin da suka shafi mata gyaran fuska ta yadda za a karfafa musu gwiwar ba da gudummawa a shirye-shiryen bunkasa jin dadin jama'a da ci gaban tattalin arziki. Nasarorin da kasar Sin ta samu ya nuna cewa, yadda aka dama da mata a harkokin jin dadin jama'a da na tattalin azriki, sun taimaka wajen daga darajarsu, da kuma ta tattalin arziki.

Na biyu, ya kamata mu kare 'yanci da muradun mata: 'Yanci da muradun mata, suna daga cikin muhimman 'yancin bil-Adam. Don haka wajibi ne a tanadi dokoki da ka'idojin da za su kare su tare da cusa su cikin dokokin kasa da akidu da al'adu, ka'idojin jin dadin jama'a. Wajibi ne mu baiwa mata damar taka rawa a cikin al'umma da harkokin tattalin arziki, tsara manufofi, ba su goyon bayan zama shugabanin a fanonin siyasa, harkokin kasuwanci da jami'o'i. Wajibi ne kuma mu tabbatar da cewa, an samar wa mata wadatattun muhimman kayayyakin kiwon lafiya, sannan a mayar da hankali ga batun samar da kayayyakin kiwon lafiya ga matan da ke yankunan karkara da kuma matan da ke da nakasa, matan da suka yi gudun hijira, masu matsakaicin shekaru da mata tsoffi da matan da suka fito daga kananan kabilu. Wajibi ne mu samar musu da makaranta tare da kare lafiyar yara mata, gina makarantun koyon sana'o'i da ilimin da mata za su iya dogara a kai har tsawon rayuwarsu don taimaka musu ta yadda za su dace da canje-canjen da ake samu a cikin al'umma da kasuwar samun aikin yi.

Na uku, kamata ya yi mu gina al'ummar da za ta dace da kowa.

Duniyar da maza da mata za su zauna a ciki tare. Al'ummar da ba a nuna wa mata bambanci ko wani nau'i na wariya. Wajibi ne mu kawar da duk wani nau'i na cin zarafin mata, ciki har da yadda ake kuntatawa mata a gida. Ya kamata mu mayar da hankali kan samar da daidaiton jinsi kana mu yi watsi da duk wata bahaguwar al'ada da ke hana ci gaban mata. A nan ina yabawa kokarin babban sakatare Ban Ki-moon kuma ina fatan sauran maza ma za su shiga wannan fafutuka.

Na hudu, ya kamata mu samar da yanayin da ya dace ga ci gaban mata a duniya. Sanin kowa ne cewa, a duk lokacin da aka samu barkewar tashin hankali, mata da kananan yara ne suka fi shan wahala. A saboda haka, wajibi ne mu tsaya tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaba da yin hadin gwiwar moriyar juna, ta yadda mata da kananan yara za su samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kamata ya yi kungiyoyin mata a kasashe daban-daban su karfafa yin mu'amala da karfafa yin abokantaka da juna, neman ci gaba tare. Ya kamata mu ci gaba da yin hadin gwiwar kasa da kasa kan batutuwan da suka shafi mata. Sannan kamata ya yi kasashen da suka ci gaba su kara tallafin kudi da fasahohin da suke baiwa kasashe masu tasowa sannan su rage gibin da ke akwai ta fuskar ci gaba tsakanin mata a kasashe daban-daban.

Abokai

Maza da mata,

Yayin da al'ummar Sinawa ke rayuwa cikin farin ciki, su ma mata na da damar su cimma burinsu na rayuwa. Kamar yadda ta tsara a cikin manufofinta, kasar Sin za ta kara daukar matakan da suka dace don karfafa daidaiton jinsi, tare da baiwa mata damar taka muhimmiyar rawa, har zuwa inda karfinsu ya kare tare da ba su goyon baya wajen ganin sun cimma burinsu na rayuwa. Mata a kasar Sin ta hanyar shirye-shiryensu na ci gaba da suka tsara, za su taka gagarumar rawa a fafutuwar da kungiyoyin mata a duniya ke yi ta yadda za su bayar da babbar gudumawa ga batun daidaiton jinsi a duniya baki daya.

A kokarin da ake na goyon bayan ci gaban mata a duniya baki daya da kuma kokarin da hukumar kula da harkokin mata ta MDD ke yi, kasar Sin a nata bangaren za ta bayar da gudummawar dala miliyan 10 ga hukumar kula da harkokin mata ta MDD saboda kokarinta na aiwatar da sanarwar Bejing da matakan da aka tsara na ganin an cimma nasarar manufofin ajandar bunkasuwa bayan shekarar 2015. A cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta agazawa wasu kasashe masu tasowa wajen gina cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara guda 100, tura tawagogin kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya, aiwatar da wasu ayyukan inganta rayuwa guda 100, don daukar nauyin kudin karatun yara mata marasa galibu da kara sanya yara mata a makaranta. Bugu da kari, kasar Sin za ta baiwa mata dubu 30 daga kasashe masu tasowa damar zuwa kasar Sin su halarci shirye-shiryen samun horo da samar da guraben samun horon sanin makamar aiki 100,000 ga al'ummomin wasu kasashe masu tasowa. Sannan a karkashin asusun da Sin da MDD suka kafa, an tanadi wasu shirye-shiryen koyon sana'o'i na musamman ga mata daga kasashe masu tasowa.

Abokai

Maza da Mata,

Ya kamata mu yi aiki kafada da kafada kana mu hanzarta gina duniyar da ta dace da mata da kuma kowa da kowa.

Ina yi wa taron shugabannin kasashen duniya fatan samun nasara.

Na gode.

(Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China