in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yin aiki tare don samar da sabon tsarin hadin gwiwa domin cin moriyar juna da nufin kyautata rayuwar al'umma da samar musu ingantacciyar makoma a rayuwar nan gaba
2015-11-03 10:19:04 cri
Xi Jinping, shugaban kasar Sin

a hedkwatar MDD dake birnin New York

a ranar 28 ga watan Satumbar shekarar 2015

Mai girma Shugaban taro

"Yan uwana Shugabanni,

A shekaru 70 da suka gabata, al'ummomin wancan lokaci sun fafata a yakin kyamar cin zali, kuma sun yi galaba a yakin da suka gudanar da harin finkarfi na Fascist, kuma sun rufe wani mummunan shafi a tarihin bil adama a duniya, a wancan yakin, an kai ruwa rana kafin daga bisani a samu galaba.

A shekaru 70 da suka gabata, al'ummar wancan lokaci sun yi hangen nesa, ta hanyar kafa Majalisar Dinkin Duniya (MDD), kuma wannan shi ne karon farko da aka kafa wata muhimmiyar hukuma ta kasa da kasa mai wakilai da kuma karfin fada a ji, wacce burinta shi ne samarwa al'umma masu tasowa kyakkyawar makoma da hada kawuna al'umma.

A shekaru 70 da suka gabata, al'ummomin wancan lokaci sun hada kai da juna, sun yi baje kolin hikimominsu, sannan suka fidda kundin daftarin dokokin MDD, wanad zai dinga yin jagoranci ga aikace-aikacen hukumar, wadanda suka dace da mnanufofin tabbatar da hadin kai a kasashen duniya. Wannan babbar nasara ce, kuma abin alfahari ne.

Mai girma Shugaban taron

"Yan uwana Shugabanni,

A ranar 3 ga watan Satumba ne al'ummar kasar Sin da takwarorinsu na kasashen duniya suka gudanar da gagarumin bikin tunawa da nasara kan yakin kyamar harin cin zalin Japan shekaru 70, da kuma nuna kyamar cin zali a duniya baki daya. Kasancewar Sin ita ce babbar kasa a gabashin Asiya, ya sa ala tilas ta sadaukar da kanta wajen tunkarar harin Japan, lamarin da ya haifar wa kasar samun hasarar rayukan mutane sama da miliyan 35. Sai dai sadaukar da kai da kasar Sin ta yi, ba ta tsaya ga kare kanta ba kadai, har ma ta taimaka wajen kawar da harin zalunci a nahiyar Turai da yankin Pasific, kuma ya kasance babbar gudumowa wanda tarihi ba zai manta da shi ba.

Tarihi dai tamkar madubi ne, kuma ta hanyar daukar darasa daga abubuwan da suka faru a baya ne duniya za ta kaucewa fuskantar irin wancan mummunan al'amarin da ya faru a baya. Dole ne mu nazarci abin da ya faru a baya duk da cewar ba za mu iya goge abin da ya riga ya faru ba, amma za mu iya daukar matakan inganta al'amurra a rayuwarmu ta nan gaba. Kuma bibiyar taririn abin da ya faru a baya ba yana nufin nuna kiyayya ba ne, sai dai kawai domin dan Adam ya tuna da darussan da ya koya kan abin da ya faru a baya domin sake aza kyakkyawan harsashin dubalin inganta rayuwar al'umma masu zuwa a nan gaba.

Mai girma Shugaban taron

"Yan uwana Shugabanni,

Cikin shekaru 70 da suka shude, MDD ta sha gwagwarmaya, dukkannin kasashen duniya sun yi kokarin tallafawa samar da zaman lafiya da gina kasashensu da samar da hadin kai. Kasancewar an kai wani sabon mataki mai cike da tarihi, akwai bukatar MDD ta yi nazari kan muhimman hanyoyin da za'a bi domin tabbatar da samun dauwamammen zaman lafiya da ci gaba a kasashen duniya a wannan karni na 21.

Wanzuwar zaman lafiya da ci gaba, su ne muhimman al'amurran da za su kawo karshen yake-yake, da magance talauci da koma baya a tsakanin al'ummar duniya.

Yunkurin tabbatar da ganin kasashen duniya na magana da murya daya, da karfafa huldar cinikayya tsakanin kasashe masu tasowa batu ne da tarihi ba zai manta da shi ba. Dunkulewar tattalin arziki duniya da ci gaban fasahar zamani, sun kara tabbatar da bude wani sabon shafi ga ci gaban duniya da kuma ba da damar gano wasu kalubalen da ya zama wajibi a tunkare su.

Bisa ga tsarin dadaddiyar al'adar Sinawa mai taken "babbar manufar ci gaban duniya ya dogara ne wajen ba da dama ga kowa ya shigo a dama dashi". Zaman lafiya, cigaba, daidaito, adalci, dimokaradiyya da 'yanci, su ne manyan muradun kowane bil Adama, kuma su ne manyan manufofin MDD.

Wadannan manufofi suna da wahalar cimmawa, dole ne sai dukkanninmu mun ci gaba da yin aiki tukuru. A bisa halin da muke ciki a wananan duniya, kowace kasa tana bukatar jingina ne da 'yar uwarta domin cimma muradi na bai daya. Ya zama wajibi mu sauya manufofinmu, donin su yi daidai da maufofin MDD, domin kulla sabuwar dangantaka da kuma tsarin mu'ammala da nufin cin moriyar juna, domin ginawa al'umma masu zuwa a nan gaba kyakkyawar makoma. To, idan dai muna bukatar cimma nasarar wadannan abubuwa da na ambata, dole ne mu mayar da hankali kan wadannan abubuwa kamar haka:

----dole ne mu gina tsarin mu'ammala tsakanin kasashen duniya ba tare da nuna fifiko ba, sannan mu rinka tuntubar juna, kuma mu fahimci juna, kuma wananan ya yi daidai da kudurin MDD na samar da daidaito. Bai kamata wata kasa don girmanta, ko ci gabanta, ko kuma karfin tattalin arzikinta, ya sa ta dinga nuna yatsa kan wata 'yar karamar kasa ko kasa mai karamin karfi ko kuma matalauciyar kasa ba. Kuma ba dace a dinga yin katsalandan kan al'amurran wata kasa ba. Wananan na nufin, kowace kasa tana da 'yanci da zabi, kan irin yanayin tsarin ci gaban da take ganin ya fi dacewa da ita. Kuma dole ne a mutunta tsarin da kasa ke amfani da shi wajen ci gaban tattalin arzikinta, da yanayin zamantakewarta, da yadda take kokarin inganta rayuwar al'ummarta. Ya kamata mu mayar da hankali kan abin da ya shafi huldar kasuwanci tsakanin kasashen duniya daban daban, ba wai tsarin kasuwanci na kasa guda ba. Ya kamata mu aiwatar da sabon tsari domin samun sakamako mai kyau, kuma mu yi watsi da tsohon tsarin da duniya ke amfani da shi a baya wanda bangare guda ne ke cin gajiyar samun riba, yayin da bangare guda ke tafka hasara, tuntubar juna wani muhimmin al'amari ne a tsarin dimokaradiyya wajen gudanar da sha'anin jagoranci da duniya ke amfani da shi. Ya kamata mu bi hanyoyin tattaunawa da juna wajen kawar da duk wasu banbance banbance da sabani dake tsakaninmu. Ya kamata mu kafa wani tsarin kawance tsakanin dukkanin kasashen duniya da na shiyya-shiyya, ta hanyar tuntubar juna a maimakon ta da jijiyar wuya, kuma mu samar da hadin gwiwwa a maimakon yin taron dangi. Ya kamata manyan kasashen duniya su yi amfani da ka'idojin hana yake-yake, da muzgunawa, kuma su tabbatar da mutunta juna, da samar da yanayi na cin moriyar juna a yayin mu'ammala a tsakaninsu. Ya kamata manyan kasashen duniya su guji nuna banbanci ga kananan kasashe, kuma su yi adalci a yayin mu'ammala da su, kuma su guji dora bukatunsu sama da bukatar kananan kasashen.

----Ya kamata mu shata wani tsari na tabbatar da tsaro, wanda zai haifar da adalci da bude kofar cudanya da juna, domin kowane bangare ya ci gajiya. A halin da duniya ke ciki na gudanar da tsarin tattalin arziki na bai daya, yanayin tsaron kowace kasa ya ta'allaka ne da na 'yar uwarta, kuma dole ya shafe ta. Babu wata kasa a duniya da za ta iya samarwa kanta cikakken tsaro ba tare da 'yar uwarta ba, sannan babu wata kasa da za ta samu zaman lafiya ta hanyar wargaza zaman lafiyar sauran kasashe. Duk wata kasa da take hankoron bin tsarin sha kai kadai, hakika tana ginawa kanta ramin halaka ne kawai. Dole ne mu yi watsi da tsarin yakin cacar baka a dukkan manufofinmu, a maimakon hakan, mu rungumi sabon tsarin bai daya na aiki tare da hadin gwiwa da juna don samar da dauwamammen tsaro. Dole ne mu yi biyayya ga manyan manufofin MDD, da manufarta kan batun tsaro domin kawo karshen tashe-tashen hankali da kuma dauwamammen zaman lafiya, sannan wajibi ne a yi amfani da hanyoyi biyu domin samar da zaman lafiya da kawar da duk wani zaman dar dar. Dole ne mu kara hada kai da juna yayin mu'amalar kasa da kasa a sha'anin tattalin arziki da zamantakewa domin tunkarar dukkan kalubalen tsaro na gargajiya da na zamani domin kaucewa yiwuwar barkewar tashin hankali.

----Dole ne mu bude kofar inganta sha'anin kirkire-kirkire, da samar da ci gaba domin ya amfanar da kowa. Abin da ya faru a shekarar 2008 na rikicin tattalin arziki da duniya ta fuskanta, ya zama abin misali da zai gwadawa duniya karuwar gibin dake tsakanin kasashe masu arziki da matalauta ba shi da alfanu, kuma abu ne marar tabbas. Don haka yana da matukar muhimmanci a gare mu mu hada hannu mu yi aiki da juna tsakanin bangarorin 'yan kasuwa da na gwamnati domin samun sakamako mai kyau da baiwa kowane bangare hakkinsa. Samar da ci gaba zai kasance mai ma'ana ne kadai, idan ya kasance an shigar da kowane bangare kuma a tabbatar an dore a kan hakan. Domin cimma wannan buri, akwai bukatar bude kofa ga kowane bangare da tallafawa juna, da samar da hadin kai. Yanayin da ake ciki a duniya a halin yanzu, kusan mutane miliyan 800 ne ke rayuwa cikin matsanancin talauci, kuma a kalla yara 'yan kasa da shekaru 5 miliyan 6 ne suke mutuwa a duk shekara, sannan kimanin yara miliyan 60 ne ba su samu damar shiga makarantu ba. A taron ci gaban kasashen duniya da MDD ta kammala kwanan nan, wanda aka cimma matsayar sabunta shirin ci gaban muradun karni na shekara ta 2015. Ya zama wajibi mu gabatar da aniyar mu, kuma mu yi aiki tare da juna domin tabbatar da ganin mun cire al'umma daga halin kuncin rayuwa da samar musu ci gaba da ingantacciyar rayuwa.

----Ya kamata mu yi kyakkyawan amfani da wayewar mu don inganta zaman lafiya, da mu'amala da kuma martaba irin banbance-banbance dake tsakaninmu. Duniya tana haska launi mai kayatarwa kasancewar cike take da al'umma masu al'adu iri daban daban. Bambancin al'umma shi ke haifar da cudanya, cudanya kuma ke haifar da fahimtar juna, fahimtar juna kuma ke haifar da ci gaba. Ta hanyar girmama juna, da fahimtar juna, da kuma zaman lafiya da juna ne duniya za ta ci gaba da rayuwa a matsayin tsintsiya madaurarki daya a tsakanin al'ummun duniya nau'i daban daban. Dole ne mu kasance muna martaba junan mu, kuma mu yi mua'ammala ba tare da nuna bambanci a tsakaninmu ba.

----Ya kamata mu gina muhallin halittu wanda a cikinsa ne muke rayuwa, kuma mu kiyaye tsirran dake cikinsa sannan mu inganta su. Ya kamata mu yi taka tsan tsan da muhallin halittu, da yadda cibiban zamani da muke samarwa na masana'antu bai yi lahani ga muhallin halittun ba, domin samun dawwamamman ci gaban bil adama a doron kasa. Gina muhallin halittu abu ne dake da muhimmanci ga rayuwar al'umma. Ya kamata al'ummomin kasashen duniya su yi aiki tare, domin gina muhallin hallitu mai inganci. Ya kamata mu martaba hallitu kuma mu kiyayya su. Kasar Sin za ta sauke irin nauyin dake wuyanta, kuma za ta ci gaba da iyakar kokarinta kan wannan al'amari. Sannan muna yin kira ga kasashen da suka ci gaba, da su daure su sauke nauyin dake wuyansu wajen rage dumamar yanayi a duniya, kuma su tallafawa kasashe masu tasowa wajen rage gurbata muhalli da shawo kan matsalar sauyin yanayi.

Mai girma Shugaban taron

"Yan uwana Shugabanni,

Al'ummar Sinawa sama da biliyan 1 da miliyan 300 sun dukufa wajen tabbatar da cimma burin sake gina hadaddiyar kasa. Kuma wannan buri na Sinawa ya ta'allaka ne da burin sauran al'ummar duniya. Ba za mu iya cimma wannan buri na Sinawa ba, har sai zaman lafiya ya wanzu a sauran sassa na duniya, sannan a samu fahimtar juna, da tallafi, da kuma goyon bayan sauran kasashen duniya. Cimma wannan burin na Sinawa, zai samar da damammaki masu tarin yawa ga sauran kasashen duniya, kuma zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a duniya da kuma ci gaba.

Kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya. A shirye muke mu tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Kasar Sin za ta ci gaba da tallafawa ci gaban duniya. Za mu ci gaba da bin hanyoyin da za su haifar da ci gaba. A shirye muke mu yi musayar kwarewar da muke da ita, da irin damammakin da muke da su da sauran kasashen duniya, kuma muna yin lale marhabun ga sauran kasashe da su zo mu hada karfi da karfe domin samar da ci gaba.

Kasar Sin za ta ci gaba da mutunta dokokin kasashen duniya. A shirye muke mu marawa ci gaban kasashen duniya baya ta hanyar hada kai da juna. Sin ita ce kasa ta farko da ta rattaba hannu kan dokokin MDD. Za mu ci gaba da kiyaye ka'idojin da ke kunshe cikin daftarin dokokin MDD. Kasar Sin za ta ci gaba da hada kai da kasashe masu tasowa. Muna goyon bayan wakilcin kasashen duniya masu tasowa a MDD, musamman kasashen nahiyar Afrika. A ko da yaushe kasar Sin tana kada kuri'ar goyon bayan kasashe masu tasowa ne.

Ina so zan yi amfani da wannan dama na sanar da cewa, kasar Sin ta yanke shawarar ware kudi dalar Amurka biliyan 1, don aiwatar da wani shirin hadin gwiwa tsakanin Sin da MDD, na samar da zaman lafiya da ci gaba na tsawon shekaru 10, domin tallafawa ayyukan majalisar dinkin duniyar da karfafa dangantaka tsakanin kasashe, da kuma bada gagarumar gudunmowa ga samar da zaman lafiya da ci gaba a duniya. Ina so na sake bayyana cewar, kasar Sin za ta marawa MDD baya a shirinta na samar da zaman lafiya, a kan haka, Sin ta yanke shawarar kafa rundunar 'yan sandan wanzar da zaman lafiya ta dindindin da kafa wata runduna ta dakarun shirin ko ta kwana mai jami'ai dubu 8. Bugu da kari ina so in sake sanar da da ku cewar, kasar Sin za ta samar da kudi dalar Amurka miliyan 100 nan shekaru 5 masu zuwa domin tallafawa dakarun kungiyar ci gaban kasashen Afrika AU, don rundunar ta AU su samu damar aikin kai daukin gaggawa a lokutan barkewar tashin hankali.

Mai girma Shugaban taron

"Yan uwana Shugabanni,

A yayin da MDD ke shiga sabon karni, ya kamata mu sake dunkulewa wuri guda, domin samar da sabuwar dangantakar hadin kai mai amfani ga ci gaban al'umma da makomar bil adam a rayuwar nan gaba. Ya kamata a samar wa duniya wani shiri na kaucewa yaki, kuma mu cusawa zukatan mu sha'awar samar da dawwamamman zaman lafiya. Ya kamata a sanya burin tabbatar da ci gaba da kuma gaskiya da adalci su yadu doron kasa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China