Yankunan da za su amfana da wadannan manufofin sun hada da jihar Xinjiang da ta Tibet da sauran yankunan kabilar Tibet dake larduna 4 a kasar.
Wadannan manufofi 20 sun hada da shirin bada ilmi a shekaru uku kafin a shiga makarantar firamare, kyautata sharudan makarantu a yankunan da ke fama da talauci, shirin kyautata abincin dalibai a makarantun kauyuka, samar da kudi ga daliban makarantun sakandare, taimakawa jihar Tibet da ta Xinjiang a fannin bada ilmi, shirin ganin dalibai sun shiga jami'o'i a yankunan da ke da talauci da dai sauransu. (Zainab)