in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin waje na kasar Rasha ya bayyana fatan yin hadin gwiwa tare da kasashen yammacin duniya don yaki da ta'addanci
2015-10-15 15:26:13 cri

A jiya Laraba, ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov ya ba da jawabi a gun taron majalisar wakilan kasar, tare da amsa tambayoyin 'yan majalisar. A ciki awa daya da aka gudanar da taron, Sergei Lavrov ya amsa tambayoyi kan harkokin siyasa da tattalin arziki da kuma diplomasiyya na kasar Rasha, musamman ma game da batutuwan da suka shafi kasashen Sham da Ukraine da kuma rahoto game da faduwar jirgin sama na kamfanin Malaysia.

A jiya Laraba, ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya ba da jawabi a gun taron majalisar wakilan kasar, inda ya bayyana cewa, kasar Rasha na gudanar da harkokin kasa da kasa bisa manufofin cikin 'yancin kai da sauke nauyin dake bisa wuyanta, hakan ya samu goyon baya da amincewa daga karin kasashen duniya. Haka kuma kasar na tsayawa kan girmama dokar duniya da kuma al'adu iri iri na duniya, ba za ta matsa lamba ga ko wane kasa don gudanar da harkokinta bisa ra'ayin kasar Rasha ba. Ya kara da cewa,

"Kasar Rasha na rika gudanar da manufar diplomasiyya bisa yancin kai domin tabbatar da mulkin kai da kuma cikakken yankin kasar. Rasha ta dauki muhimmin matsayi a duniya, ta ba da gudummawa mai yakini ga daidaitowar hulda a tsakanin kasa da kasa. Mun girmama hanyoyi iri iri da kasashen duniya suka zaba wajen raya kansu, ba mu matsa musu lamba ko kadan ba, shugaban kasar Putin shi ma ya jaddada cewa, ba wadda ke da nauyin bin hanyar da sauran kasashe suka zaba mata wajen neman samun bunkasuwa."

Sergei Lavrov ya ce, shugaban kasar Putin ya tantance yanayin duniya sau da dama, kuma ya gabatar da hakikanan matakai da nufin kawo karshen rikicin shiyya-shiyya da kuma batutuwan duniya a gun taron MDD karo na 70. Domin tinkarar kalubalolin da kungiyoyin ta'addanci suka kawo wa kasashen duniya, kasar Rasha ta yi hada kai tare da kasashe da dama don yaki da ta'addanci, kuma ya ba da shawara ga kwamitin sulhu wajen kafa kawancen yaki da ta'addanci, amma kasashen yammacin duniya ba su mayar da martani a kai ba. A game da haka, ya ce,

"Shugaban kasar Rasha Putin ya yi kira da a yi hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, kana da hada kai tare da kasashen dake fama da ta''adanci bisa dokokin duniya. Sannan Kasar ta taba ba da shawarar kafa kawancen yaki da ta'addanci a gun taron kwamitin sulhu na MDD, amma kasashen yammacin duniya ba su son tattauna wannan batu bisa wasu dalilan da kowa ya sani."

Game da labarin da kafofin watsa labarum kasashen yammacin duniya suka bayar, wato bayan da kasar Rasha ta kai farmakin sama ga kungiyar IS dake kasar Sham, sojojin saman kasar kuma sun murkushe manyan ayyukan kungiyar adawa ta kasar Sham, Sergei Lavrov ya bayyana cewa, sojojin kasar sun kafa cibiyar musayar ra'ayi tare da sojojin kasashen Sham da Iraki da kuma Iran, domin musayar labaran leken asiri, domin inganta aikin yaki da 'yan ta'adda. A game da labarai maras gaskiya da kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya suka bayar, sojojin kasar Rasha sun ba da sharudan bidiyo da dama, wadanda suka bayyana cewa, dukkan wuraren da kasar Rasha ta kai farmaki a kai su ne sansanonin 'yan ta'adda.

Ban da haka kuma, Sergei Lavrov ya ce, halin da ake ciki a gabashin kasar Ukraine ya rika jawo hankulan kasashen duniya, kasar Rasha ta yi imani da cewa, daukar matakan soja ba zai kawo karshen rikici ba, ya kamata bangarori daban daban su bi yarjejeniyar Minsk domin tsara shirin daidaita batu ta hanyar yin shawarwari.

Bugu da kari, Sergei Lavrov ya mai da martani ga rahoto game da faduwar jirgin sama na kamfanin Malaysia da aka bayar a ranar talata 13 ga wannan wata, ya ce, firaministan kasar Holland ya kalubalanci kasar Rasha da ta bi rahoton da kwamitin tsaron kasarsa ya bayar kan wannan hadari, amma yana fatan kasar Holland za ta tantance sakamakon bincike da kamfanin Almaz-Antei na kasar Rasha ya samu. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China