in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun sauye-sauye ga salon raya tattalin arzikin Sin
2015-10-09 19:07:20 cri
Yayin da shugabar asusun ba da lamunin duniya IMF Christine Lagarde ke halartar taron shekara-shekara na asusun a lokacin kaka da aka shirya a birnin Lima hedkwatar kasar Peru a jiya Alhamis 8 ga wata, ta ce, yanzu, yawan raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya yi daidai da yadda ake zato, kuma wannan zai yi amfani ga raya tattalin arzikin kasar cikin dogon lokaci.

Madam Lagarde ta ce, Sin na canja salon raya tattalin arzikinta yanzu wato tana sa kaimi ga sayayya don samun saurin bunkasuwar tattalin arziki kamar yadda ake gani, lalle ta yi rawar gani. Kazalika ta ce, ba za a iya rasa tangal-tangal wajen raya tattalin arziki ba yayin da take canja salon raya shi, sabo da babu wata kasa da za ta iya canja salon raya tattalin arikinta, ba tare da samun tasiri game da saurin bunkasuwar tattalin arzikinta ba.

A cikin wata shawarar da IMF ta fidda kwanan baya, an ce, yawan raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya yi daidai da yadda ake zato, kuma Sin na canja salon raya tattalin arziki don raya shi cikin dogon lokaci da tsanaki, ana ganin cewa, bayan da Sin ta kara yin kwaskwarima game da kasafin kudi, da inshora da masana'antun gwamnati, kasashen duniya za su ci gajiya daga sauye-sauyen da take samu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China