in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yaba wa 'yar kimiyyar Sin Tu Youyou da ta lashe kyautar lambar yabo ta Nobel
2015-10-09 12:26:35 cri

An tace sinadarin artemisinin ne daga magungunan gargajiyar kasar Sin, kuma yanzu haka an yi amfani da sinadarin wajen shawo kan cutar malariya, har ya ceci rayuwar jama'ar kasashen Afirka masu fama da cutar sama da miliyan daya.

Lokacin da aka sanar da labarin cewa, likitar kasar Sin Tu Youyou ta lashe kyautar lambar yabo ta Nobel ta ilmin ba da jiyya ta bana, nan take daraktan hukumar kiwon lafiya da shirin tsara iyali ta kasar Sin Li Bin ta taya Tu Youyou murna, ta ce, "Tu Youyou ta yi nasarar lashe kyautar lambar yabo ta Nobel sakamakon shekaru da dama da ta kwashe, tana kokarin nazari kan magungunan gargajiyar kasar Sin, wannan shi ne karo na farko da ta tace sinadarin artemisinin wanda a halin yanzu ake amfani da maganin da aka hada da sinadarin wajen shawo kan cutar malariya, masu aikin ba da jiyya na kasar Sin suna alfahari da wannan ci gaba da aka samu, ganin yadda magungunan gargajiyar kasar Sin suka ba da babbar gudummuwa ga aikin kiwon lafiyar dan Adam, ban da haka kuma nazarin zai kara ingiza hadin gwiwar harkokin kiwon lafiya tsakanin Sin da Afirka."

Kungiyoyin kasa da kasa da jami'an kiwon lafiya na kasashen Afirka da suka halarci taron su ma sun taya Tu Youyou murna, daraktar yankin Afirka ta hukumar kiwon lafiya ta duniya Tshedi Moeti ta bayyana cewa, tace sanadarin artemisinin daga maganin gargajiyar kasar Sin lamari ne da ya faranta ran mutane, ko shakka babu zai tamaka wajen ci gaban aikin kiwon lafiya a Afirka, har ma a fadin duniya baki daya. Moeti ta ce, "Sinadarin artemisinin zai kawo babban sauya a bangaren aikin kiwon lafiyar kasa da kasa, musamman ma a nahiyar Afirka, saboda jama'ar kasashen Afirka, musamman ma yara sun fi shan fama da cutar malariya."

A shekarar 1972 ne, Tu Youyou da abokan aikinta suka fara aikin tace sinadarin artemisinin daga wani irin nau'in maganin gargajiyar kasar Sin wato artemisia carvifolia, daga nan ne aka fara yin amfani da magungunan gargajiyar kasar Sin wajen shawo kan cutar malariya, kuma masanan kimiyyar kasar Sin a fannin ba da jiyya suna ci gaba da yin kokari kan wannan. A shekarar 1998, jami'ar koyon aikin likita ta hanyar yin amfani da magungunan gargajiyar kasar Sin ta birnin Guangzhou na lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin ta fara gudanar da aikin yin nazari kan magani mai inganci da aka hada da sinadarin artemisinin, ya zuwa shekarar 2004, maganin ya samu kyautatuwa matuka, an kuma fara amfani da maganin a tsibirin Komoros na Afirka ne a shekarar 2007, maganin ya ba da mamaki matuka saboda adadin wadanda suka kamu da cutar malariya a kasar ya ragu da kashi 98.7 bisa dari cikin watanni uku kacal. Kana a shekarar 2014, babu wanda ya rasa ransa sakamakon cutar a duk fadin kasar da ke nahiyar ta Afirka.

Wannan magani mai inganci zai iya shawo kan cutar malariya cikin sauri, mai fama da cutar zai samu warka bayan ya sha maganin sau biyu kawai, shi ya sa ana iya cewar, maganin ya dace da dukkan jama'ar kasashen duniya.

Mataimakin shugaban kasar Komoros, kuma ministan kiwon lafiyar kasar Fouad Mohadji ya ce, "A baya, iyalaina guda uku sun taba kamuwa da cutar malariya, kullum su kan je asibiti, kuma suke kashe kudi da yawa. Amma bayan shekarar 2007, wato bayan da aka fara yin amfani da maganin na kasar Sin, dukkanin jama'ar kasar sun samu sa'ida daga wannan wahalar, ana iya cewa, sakamakon haka, ba ma kawai a fannin kiwon lafiya ba, har ma a fannin bunkasuwar zamantakewar al'umma, kasar ta Komoros ta samu ci gaba sosai."

Yanzu haka yawan mutanen da suke mutuwa a ko wace shekara a fadin duniya sakamakon cutar malariya ya kai miliyan 4 da dubu dari uku, a cikinsu, kashi 90 bisa dari sun fito ne daga nahiyar Afirka, kuma yawancinsu yara ne da ba su kai shekaru 5 da haihuwa ba. Sakamakon nasarar da Tu Youyou da abokan aikinta suka samu wajen tace sanadarin artemisinin, ana fatan zai taimaka wajen kawo karshen cutar Malariya, kuma masu aikin ba da jiyya na kasar Sin za su ci gaba da yin kokari wajen ganin bayan cutar kwata-kwata. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China