in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin CGCOC dake Najeriya ya ba da tallafin kayayyakin ga wadanda bala'in ambaliyar ruwa ya shafa.
2015-10-09 10:47:50 cri

A jiya Alhamis, kamfanin CGCOC na kasar Sin dake Najeriya ya tura jami'an bada tallafi zuwa jihar Kogi dake tsakiyar kasar, inda ake fama da bala'in ambaliyar ruwa.Kamfanin ya ba da kayayyakin tallafi wadanda aka kiyasta kudin su ya kai naira miliyan 2 ga gwamnatin jihar.

 

Tun farawar daminar bana, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu yankunan kasar, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa a sassan kasar da dama, kuma jihar Kogi dake gabar kogin Niger ta fuskanci bala'i mai tsanani, inda hanyoyi da kuma gidaje suka lalace a sakamakon ambaliyar.

Domin tallafawa al'ummar da bala'in ya shafa, kamfanin CGCOC dake Najeriya ya kai dauki cikin gaggawa ta hanyar ba da kayayyakin tallafi da suka hada da shinkafa da taliya mai saukin dafuwa da filawa da man girki da kuma sukari.

A yayin bikin mika kayayyakin tallafin a jiya Alhamis, mataimakin gwamnan jahar Kogi, ya nuna godiya ga kamfanin na kasar Sin, ya kuma yi alkawarin cewa, za a ba da kayayyaki ga mutanen da bala'in ya shafa. Shugaban kamfanin CGCOCO ya bayyana cewa, kamfanin na kasar Sin dake Najeriya ya dauki wannan mataki ne domin biyan bukatun mutanen da bala'in ya ritsa da su.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China