in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka sun gabatar da hadaddiyar sanarwa kan sauyawar yanayi
2015-09-28 14:19:34 cri

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake ziyara a kasar Amurka, Sin da Amurka sun gabatar da wata sabuwar hadaddiyar sanarwa kan sauyin yanayi. A cewar masana, wannan sanarwa za ta samar da gudummawa ga babban taron sauyin yanayi na birnin Paris da yunkurin cimma yarjejeniyar yanayi ta duniya cikin adalci.

An gabatar da hadaddiyar sanarwa kan sauyin yanayi a wannan karo ne bayan da aka taba gabatar da irin wannan sanarwa a cikin watan Nuwanba na shekarar 2014 a tsakanin shugabannin kasashen biyu a birnin Beijing. Sanarwar ta yi nuni da cewa, kasashen biyu sun yi imani da yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen cimma daidaito a taron sauyin yanayi da za a gudanar a birnin Paris na kasar Faransa, da kuma aiwatar da ayyukan da aka tsara yayin da ake yin la'kari da cimma burin kiyaye dumamar yanayin duniya a kasa da digirin Celcius 2.

Mataimakin shugaban cibiyar nazarin sauyin yanayi da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin Zou Ji ya bayyana wa 'yan jarida cewa, an kara zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka a fannin sauyin yanayi bisa hadaddiyar sanarwar a wannan karo. Ya ce,

"An kara zurfafa tunanin daukar alhaki tare amma akwai bambanci. A bara, an amince da irin wannan tunanin kawai, amma a bana ana bukatar ganin an aiwatar da wannan tunanin yadda ya kamata. Kana a wannan karo, kasashen biyu sun jaddada muhimmancin kawo haske ga ayyukan kiyaye muhalli na duniya don kara yin imani da amincewa da juna."

Game da kudaden da za a kebe domin aiwatar da ayyukan, Sin da Amurka sun jaddada cewa, kasashe masu ci gaban tattalin arziki sun yi alkawarin tattara dala Amurka biliyan 100 a kowace shekara tun daga yanzu har zuwa shekarar 2020 don biya bukatun kasashe masu tasowa. Amurka ta jaddada cewa, za ta bada kudi dala biliyan 3 ga asusun kiyaye yanayi, kana Sin ta sanar da samar da kudin Sin Yuan biliyan 20 don kafa asusun hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa kan tinkarar sauyin yanayi don nuna goyon baya ga sauran kasashe masu tasowa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi.

Tun daga lokacin bazara na shekarar bana, masanan Sin da Amurka sun yi shawarwari sau da dama kan manufofin tinkarar sauyin yanayi da sauran batutuwa don bada shawara ga shugabanninsu. Malam Zou Ji ya zama mai kula da wannan aiki na bangaren kasar Sin. A ganinsa, Sin da Amurka sun cimma daidaito a fannin samar da kudi da sauransu, lamarin da zai samar da gudummawa ga cimma yarjejeniya game da sauyin yanayi a karshen shekarar bana a birnin Paris. Zou Ji ya bayyana cewa,

"Hadaddiyar sanarwa sakamako ne na shawarwari a tsakanin Sin da Amurka, wadda ta bayyana daidaiton da kasashen biyu suka cimma game da yadda za a cimma yarjejeniya a birnin Paris, kana za ta sa kaimi ga cimma yarjejeniyar."

Game da tinkarar sauyin yanayi a cikin kasar Sin, alkawarin da Sin ta gabatar ya jawo hankali sosai. A cikin hadaddiyar sanarwar, an ce, Sin za ta rage yawan iskar Carbon Dioxide da ake fitar da kashi 60 zuwa 65 cikin dari a shekarar 2030 bisa na shekarar 2005. Mataimakin shugaban kwamitin masanan sauyin yanayi na kasar Sin He Jiankun ya bayyana cewa, wannan ya bayyana cewa, ana bukatar Sin ta kara yin kokari wajen cimma wannan buri idan aka kwantanta ta da kasashe masu ci gaba. Malam He Jiankun ya bayyana cewa,

"An hana karuwar yawan fitar da iskan Carbon Dioxide, hakan na bayyana cewa an hana kara yin amfani da makamashin kwal, da man fetur, tare da bukatar kara yin amfani da makamashin karfin ruwa, iska, hasken rana da nukiliya. Wannan na bukatar da kara samar da wutar lantarki kilowatt miliyan 20 ta karfin iska, kilowatt miliyan 20 ta hasken rana, kilowatt miliyan 10 ta nukiliya. Sharadin nan duk wata kasa mai sukuni ba ta cimma ba tukuna. Don haka, wannan ya fi wuya ga kasar Sin."

Hakazalika kuma, kasar Sin za ta kaddamar da tsarin yin ciniki kan izinin fitar da hayakin Carbon a dukkan fadin kasar a shekarar 2017, wanda zai shafi sha'anonin karfe, wutar lantarki, sarrafa sinadirai, gine-gine, samar da takardu, karafan da ba su dauke da bakin karfe a cikinsu da dai sauransu. A ganin Zou Ji, kafa irin wannan tsari da sauran matakai sun nuna sahihancin kasar Sin na rage yawan Carbon da ake fitarwa. Zou Ji ya bayyana cewa,

"Ana bukatar ayyuka da dama wajen raya kasuwar Carbon ta kasar Sin. Wannan sabon tsari ne, wanda ke bukatar a gudanar da ayyuka da yawa a nan gaba. Amma mun yi niyyar raya shi, domin idan ba a aiwatar da matakin yadda ya kamata ba, watakila za a kasa cimma burin shekarar 2020 da na 2030 da muka tsara." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China