Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Afrika ta kudu Maite Nkoana-Mashabane da suka sanar da hakan tare, sun ce shugabannin kasashen biyu duk sun amince a daga matsayin taron ministocin na hadin gwiwwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika karo na 6 zuwa babban taron.
Shugabannin kasashen guda biyu har ila yau za su gayyaci sauran shugabannin kasashen Afrika da su halarci taron wanda zai gudana a ranakun 4-5 na watan Disamban bana. (Fatimah Jibril)