in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta shirya gagarumin biki don tunawa da cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kin harin Japan
2015-09-03 15:01:48 cri

Da karfe 10 na safiyar yau ne aka fara kasaitaccen bikin cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu inda aka harba bindigogin jinjinawa sau 70, tare da daga tutar kasar Sin, kana daga bisani dukkan mahalarta bikin suka fara rera taken kasar Sin.

A ranar 2 ga watan Satumbar shekarar 1945 ne, mayakan kasar Japan suka sa hannu kan takardar mika wuya, lamarin da ya nuna nasarar da aka samu a kan mayakan kasar Japan da kuma kawo karshen yakin duniya na biyu. Kasancewar ta yankin da ya fi fuskantar yakin, kasar Sin ta samar da babbar gudummawa a yakin duniya na biyu, haka kuma, a yakin da kasar Sin ta yi da mayakan kasar Japan, yawan Sinawan da suka ji raunuka ko suka mutu ya kai sama da miliyan 35, baya ga kudade kimanin dala biliyan 100 da aka yi hasara. A shekarar 1951, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin mai da ranar 3 ga watan Satumba a matsayin ranar tunawa da narasar da Sinawa suka samu a kan mayakan kasar Japan. A shekarar 2014 kuma, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta kafa dokar dake tabbatar da ranar 3 ga watan Satumba a matsayin ranar tunawa da nasarar da jama'ar kasar Sin suka cimma kan yaki da mayakan kasar Japan.

A yau 3 ga watan Satumban da muke ciki, tsofaffin shugabanni da shugabanni masu ci na kasar Sin, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon da wasu shugabannin kasashen duniya, da na kungiyoyin kasa da kasa da shiyya-shiyya kimanin guda 60 ne suka halarci kasaitaccen bikin da kasar Sin ta shirya a nan birnin Beijing. Shugaba Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a yayin bikin, inda ya nuna cewa, yaki tamkar madubi ne. kallonsa kan sa a kara fahimtar muhimmancin zaman lafiya. Don haka ya zama wajibi ga jama'a su rungumi darussan dake kunshe cikin tarihi, a kuma zage damtse wajen tabbatar da zaman lafiya. Ya kara da cewa,

"Domin wanzar da zaman lafiya, ya dace mu yi hadin gwiwa wajen samar da duniya mai burin cimma makoma guda. Kyama, da kiyayya, da yaki ba sa haifar da komai sai masifa da halin kunci, yayin da martaba juna, da daidaito, da zaman lafiya, da ci gaba, da kyakkyawar makoma ke matsayin ingantacciyar hanyar da ya dace a bi. Ya zama wajibi dukkanin kasashe su hada gwiwa da juna, wajen tabbatar da nasarar ka'idoji da tsare tsare wadanda ke kunshe cikin dokokin MDD, su kuma kafa wani sabon tsarin hulda na kasa da kasa, wanda zai ba da damar cimma moriyar juna, da babbar nasarar wanzar da zaman lafiya da ci gaba mai dorewa. "

Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana. Ya ce,

"Mu Sinawa mutane ne masu kaunar zaman lafiya. Kuma duk ci gaban da kasar Sin ta samu ba za ta mamaye wata kasa ko ta zama barazana ko kuntatawa wata kasa ba. Burin Sinawa a kullum shi ne kulla huldar abokantaka da dukkan kasashe tare da nuna sakamako ko nasarar da Sinawa suka samu kan mayakan kasar Japan da kuma masu nuna ra'ayin nuna karfin tuwo a duniya sannan da samar da babbar gudumawar da ta bayar a duniya ga ci gaban bil-Adama."

A matsayin wani muhimmin bangare na gagarumin bikin tunawa, bikin faretin soja ya jawo hankalin mutane sosai. Bikin faretin soja na wannan karo ya sha bamban da sauran bukukuwan faretin soja da kasar Sin ta taba gudanarwa don muryar kafuwarta, wanda ya zama karo na farko da aka yi don tunawa da samun nasarar yakin kin harin Japan. Yayin da yake kallon faretin sojan, Shugaba Xi Jinping sanye da riga mai kwala irinta marigayi Chairman Mao ya shiga wata mota kirar Red Flag, ya bi hanyar Chang'an don kallon rukunonin soja 11 da rukunonin na'urorin yaki 27.

Domin jaddada muhimmancin taken bikin tunawa, da farko da jerin jiragen sama masu saukar angulu a sararin samaniya suka fitar da alamar lamba 70 wanda ke bayyana shekaru 70 na kawo karshen yakin duniya na 2. wadansu jiragen guda 7 na biye da su suna fitar da hayaki masu launukan ja, ruwan kwai da shudi

Bikin faretin soja da aka nuna a yau ya kunshi rukunoni biyu na tsoffin sojoji da suka fafata a yakin kin harin Japanawa, da rukunoni 11 na sojoji da ke tafiya a kasa, da rukunoni 17 na sojojin ketare, da rukunoni 27 na na'urorin soja, da rukunoni 10 na jiragen saman yaki. Don haka gaba daya yawan sojojin da suka shiga faretin ya zarce dubu 10, yawan na'urorin sojin kasar ya kai sama da 500, yayin da akwai jiragen saman yaki nau'o'i daban daban kimanin 200.

Abin da ya kamata a lura shi ne, wannan shi ne karon farko da tsoffin sojojin da suka shiga yakin kin harin Japanawa suka shiga wannan fareti, baya ga gayyatar sojojin ketare domin shiga wannan faretin, lamarin da ya sheda girmamawar da aka nuna wa sojoji masu fafata a fagen yakin, da kuma muhimmiyar ma'anar tarihi na wannan bikin tunawa. Har ila shi ne karon farko, da sojojin za su gabatar da fareti bisa tsarin ayyukan da suke gudanarwa a fagen daga, wanda ya sheda hadin gwiwar da za a yi koda yaki ya barke a nan gaba. Bugu da kari, na'urorin da aka nuna a bikin muhimman na'urorin yaki ne da kasar Sin ta kera da kanta, kana wannan shi ne karon farko da aka gabatar da kashi 84 cikin dari na wadannan na'urori a bainar jama'a. Game da jiragen saman yaki da suka shiga faretin, akwai sabbin nau'o'i daban daban da aka nuna a bainar jama'a a karon farko.

Yayin kammalar bikin tunawa, balan-balan dubu 70 da kuma tantabaru dubu 70 sun tashi zuwa sama domin nuna cewa, jama'ar kasar Sin za su hada gwiwa tare da al'ummar duk duniya wajen wanzar da zaman lafiya. (Kande Gao, Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China