in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga samun zaman lafiya da bunkasuwa mai dorewa a gun taron shugabannin majalisun dokokin kasashen duniya karo na 4
2015-09-03 09:50:22 cri
An rufe taron shugabannin majalisun dokokin kasashen duniya karo na 4 a cibiyar MDD dake birnin New York a jiya ranar 2 ga wata, inda aka zartas da sanarwa cewa, an yi kira da a yi kokarin warware kalubalen duniya, da sa kaimi ga aiwatar da sabuwar ajandar samun bunkasuwa, da kuma jaddada muhimmancin tunawa da cika shekaru 70 da nuna fin karfin Fascit da kafuwar MDD.

Sanarwar ta bayyana cewa, shugabannin majalisun dokokin kasa da kasa sun yi imani da samar da gudummawa wajen warware kalubalen duniya, da yin kira da a warware matsaloli ta hanyar yin shawarwarin siyasa, da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu wajen yaki da ta'addanci. Kana sanarwa ta bayyana ra'ayi game da batutuwan kawar da makaman nukiliya, yaki da manyan laifuffuka, 'yan gudun hijira da bakin haure, sauyin yanayi, raya dokokin kasa da kasa da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China