in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Yuanchao ya gana da ministan harkokin wajen Kongo Kinshasa
2015-07-30 18:29:37 cri

A jiya Laraba ne mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao, ya gana da ministan harkokin waje da na hadin gwiwa da kasashen duniya na kasar Kongo Kinshasa Raymond N'Tungamulongo a nan birnin Beijing.

Yayin zantawar tasu, Mr. Li ya ce kasar Sin na dora muhimmancin gaske kan raya dangantaka tsakaninta da Kongo Kinshasa. Tana kuma fatan ci gaba da hadin gwiwa da kasar a fannin tsarin raya kasa, da zurfafa hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, duka da nufin cimma moriyar juna, a kokarin sa kaimin daga matsayin dangantakar su zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, Mr. N'Tungamulongo, cewa ya yi kasar Sin aminiya ce ga Kongo Kinshasa. Kana kasar na matukar godiya ga Sin, bisa taimakonta cikin dogon lokaci. Ya kuma yi fatan za a zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a duk fannoni domin cimma moriyar juna. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China