in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yaba kokarin 'yan sandan Sin na tabbatar da tsaro a bikin ranar samun 'yancin kan Liberia
2015-07-30 13:12:24 cri

Daga ranar 26 zuwa 27 ga wata ne, aka gudanar da wani kasaitaccen biki a babban birnin jihar Sinoe, Greenville, domin murnar cika shekaru 168 da samun 'yancin kan kasar Liberia. Kamar yadda tawagar musamman ta MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Liberia wato UNMIL ta shirya, an tura rukuni na uku na rundunar 'yan sandan kwantar da tarzoma ta kasar Sin, kana runduna daya tilo ta 'yan sandan kiyaye zaman lafiya da MDD ta aike zuwa jihar Sinoe don gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya da yin mu'amala a yayin bikin yadda ya kamata. Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf, mukaddashin wakilin musamman na UNMIL Antonio Vigilante, jakadan Sin dake kasar Liberia Zhang Yue, da kuma bangarori daban daban da suka halarci bikin sun nuna yabo ga 'yan sandan kasar Sin.

Bikin murnar cika shekaru 168 da samun 'yancin kan kasar Liberia biki mai girma da ya kunshi ayyuka da dama da aka gudanar, kana ya jawo hankali sosai. Jami'in mai kula da harkokin siyasa na rukuni na uku na rundunar 'yan sandan kiyaye zaman lafiya ta Sin Li Peisen ya yi bayani cewa, rukuninsa ya gudanar da bincike tare da tsara shirin aikin tabbatar da tsaro a bikin ranar samun 'yancin kan Liberia, kana sun gudanar da sintiri a birnin Greenville da yankunan dake kewayensa, da yin bincike kan yanayin tsaro, sun kuma kara yin atisaye don inganta dabarunsu na tinkarar duk wata matsala da ka iya kunno kai. A yayin bikin, rukunin 'yan sandan ya kuma gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a dandalin da ake gudanar da bikin, tabbatar da tsaron tawagar UNMIL da jakadun kasashe 19, da kuma wakilan hukumomin kasa da kasa. Kana sun kimtsa tsaf ta fuskar ayyukan soja don tabbatar da cewa, bikin ya gudana yadda ya kamata.

A Litinin ne, shugaban rukuni na uku na rundunar 'yan sandan kwantar da tarzoma ta kasar Sin Zhang Guangbao ya yi wa shugabar kasar Liberia Sirleaf bayani game da ayyukan rundunar, kana a madadin rundunar, Mr Zhang ya taya ta murnar cika shekaru 168 da samun 'yancin kan kasar ta Liberia.

A jawabinta, shugaba Sirleaf ta bayyana cewa, rundunar 'yan sandan kwantar da tarzowa ta kasar Sin ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Liberia, don haka a madadin gwamnatin kasar Liberia da jama'arta, ta nuna godiya ga rundunar.

A ranar Lahadi ne, mukaddashin wakilin musamman na tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a Liberia UNMIL Antonio Vigilante ya isa birnin Greenville, inda ya yi shawarwari tare da shugabannin rundunar 'yan sandan kwantar da tarzowa ta kasar Sin da jakadun kasa da kasa dake kasar Liberia da kuma wakilan hukumomin kasa da kasa, inda Vigilante ya nuna yabo ga ayyukan rundunar 'yan sandan kasar Sin, ya ce rundunar ta zama abin misali da ya kamata sassan UNMIL su koyi fasahohi daga wajenta. Ya kuma yi nuni da cewa, tun lokacin da rukuni na uku na rundunar 'yan sandan kasar Sin ya isa yankin aiki, ya kasance mai bin ka'idojin MDD na tabbatar da adalci da girmama bambance-bambance, da yin namijin kokarin gudanar da ayyukansu. Kana sun yi kiran da a kafa tsarin hadin gwiwa a tsakanin sojoji da 'yan sanda karo na farko a tawagar UNMIL, wanda ya kasance sabon tsarin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na UNMIL, da kuma ba da gudummawa sosai wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar Liberia.

Ban da wannan kuma, a yayin bikin, jakadan Sin dake kasar Liberia Zhang Yue ya je sansanin rukuni na uku na rundunar 'yan sandan kwantar da tarzoma ta kasar Sin, inda ya duba na'urori da yanayin da sansanin rundunar ke ciki, kana ya saurari rahoton da jami'i mai kula da harkokin siyasa na rundunar Li Peisen ya gabatar game da ayyukan rundunar. Jakadan Zhang Yue ya bayyana cewa, yana sane da yabon da gwamnatin kasar Liberia da jama'arta, da manyan jami'an tawagar UNMIL da dukkan sojoji da 'yan sandan kiyaye zaman lafiya suka yi wa rundunar 'yan sandan kwantar da tarzoma ta kasar Sin, inda suka bayyana rundunar a matsayin wadda ta fi kwarewa da inganci cikin tawagar UNMIL. Yana mai alfahari da wadannan kalamai. Jakada Zhang ya kara da cewa, rukuni na 3 na rundunar ita ce ke wakiltar 'yan sandan kiyaye zaman lafiya na kasar Sin, kuma kasar Sin tana alfahari da ita. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China