in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari kan ofishin jakadancin Nijar dake Masar
2015-07-29 18:27:20 cri

Kamfanin dillancin labaru na MENA ya bayyana aukuwar wani hari a ofishin jakadancin jamhuriyar Nijar dake kasar Masar.

Kamfanin dillancin labarun ya ce harin na yau Laraba, ya yi sanadiyyar mutuwar mai gadi daya, yayin da kuma wasu mutane biyu suka ji rauni.

Wani jami'in hukumar tsaron kasar ta Masar ya tabbatar da hakan, inda ya ce da sanyin safiyar Larabar nan ne wasu mahara uku da ba a san ko su wane ne ba, suka bude wuta kan masu gadin dake gaban ofishin, lamarin da ya haddasa mutuwar mai gadi daya, yayin da sauran mutanen dake wurin su biyu suka jikkata.

Yanzu haka dai an rufe ofishin jakadancin na Nijer, kana 'yan sanda sun sanya shinge a titunan dake kewayen wurin domin gudanar da bincike.

Kawo yanzu babu wata kungiya ko mutum guda da ya sanar da daukar alhakin kaddamar da harin.

Tun dai lokacin da rundunar sojan Masar ta hambarar da tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi daga mukaminsa a watan Yuli na shekarar 2013, masu tsattsauran ra'ayi suka maida zirin Sinai a matsayin sansaninsu, inda suke ci gaba da kaddamar da hare-hare a wurare daban daban, ciki hadda wasu muhimman wurare kamar birnin Alkahira da dai sauransu.

A wasu lokuta, irin wadannan mayaka kan kai hari kan wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje dake kasar ta Masar.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China