in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ina aka kwana don kawar da kungiyar Al-Shabaab ta Somaliya?
2015-07-29 11:13:18 cri

A ranar Talata ne shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya yi kakkausar suka game da harin kunar bakin waken na ranar Lahadi da kungiyar Al-shabaab ta Somaliya ta kai, harin da ya haddasa mutuwar wani jami'in tsaro na ofishin jakadancin Sin da ke kasar da ma wasu mutane da dama. Manazarta sun bayyana cewa, yadda kungiyar ke ci gaba da kaddamar da hare-hare, muddin bangarorin daban-daban ba su hada gwiwa tare ba, zai yi matukar wahala a kawar da wannan kungiya.

An kai harin ne a wani otel mai suna Jazeera da ke birnin Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, kuma bayanai na nuna cewa, abin da mutum ke iya gani a wurin shi ne tarkacen motoci da sauran kayayyaki da suka kone kurmus warwatse a gaban otel din, kuma 'yan kwana-kwana na kwashe duwatsun da suka watsu ta ko'ina sanadiyar bama-bamai da suka fashe a cikin otel din, kuma har yanzu abubuwa ba su koma dai-dai a otel din ba.

Bayanan da yan sanda suka bayar na nuna cewa, wani mahari ne, ya ta da bam din da aka dasa cikin wata mota da ke gaban otel din, kuma karfin fashewar bam din ya sa wasu gine-ginen da ke kusa da wurin sun rugurguje, kuma yawancin mutanen da suka mutu fararen hula ne. Yanzu haka dai 'yan sanda sun killace wurin da ma sauran titunan da ke kusa da wurin, don gudanar da aikin ceton wadanda lamarin ya shafe tare da gudana da binciken lamarin, kana an kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin da ke kusa da wurin, ko da yake ya zuwa yanzu an kammala kwashe gawawwakin mutanen da harin ya rutsa da su.

Wata majiyyata ta ce, an yi amfani da wata babbar mota ce wajen jigilar bam din da ya kai Ton guda don kai harin, ta wani wuri da babu wata katanga mai karfi da ta kewaye otel din, yawan mutanen da suka mutu ko jikkata zai ci gaba da karuwa. Wani ma'aikacin otel din mai suna Abdi Dipu ya ce, tashin bam din ya yi kama da girgizar kasa, inda mutane suka rika yin kururuwa don neman tsira da rayukansu.

Wani kwararre a fannin tsaro na kasar Kenya Fred Neyabella ya ce, mayakan kungiyar Al-Shabaab sun sake kai hare-hare kan fararen hula ne sakamakon fatattakar da sojojin gwamnatin Somaliya suka musu, domin su ta da zauna-tsaye da kuma nuna karfin kungiyar.

Shi kuwa, shehu malamai a jami'ar Ummah ta kasar Kenya Hassan Muandewa yana ganin cewa, wannan hari ya yi kama da sauran hare-haren da aka kai a baya, a hannu daya kuma sun yi hakan ne a matsayin ramuwar gayya, a dayan hannu kuma, sun yi hakan ne don shaida cewa, mambobin kungiyar na iya shiga kowanne unguwanni, kuma za su iya kai hare-hare a ko da yaushe.

Tun lokacin da aka fatattaki mayakan kungiyar daga wuraren da ta kame a Mogadishu babban birnin kasar da kuma Kismaayo wato muhimmin gari a kudancin kasar a shekarar 2012. Daga bisani kuma, wannan kungiyar ta sha kai hare-hare a kasar Somaliya da Kenya da ke makwabtaka da ita, kuma ana ganin cewa, da wahala a gane su wanene mambobin kungiyar.

Haka kuma, manazarta sun bayyana cewa, duk da cewa, bangarorin daban-daban na kokarin ganin bayan kungiyar, amma har yanzu kungiya tana nan daram, kuma wannan bai rasa nasaba da yanayin da ake ciki a kasar Somaliya.

Tun shekarar 1991 ne rikici ya barke a kasar Somaliya, kuma tattalin arziki ya samu koma baya, a halin da ake ciki yanzu, kungiyar ta yi amfani da yanayin kuncin da jama'a ke ciki da addini, wajen yiwa jama'a alkawari, wai za su samar da tsaro da farfado da tattalin arziki, kuma ta samu wasu magoyan baya.

Neyabella ya yi nuni da cewa, kungiyar ta'addancin ta yi kaurin suna wajen tayar da rikici cikin shekaru sama da 20 da suka gabata a kasar, yana mai cewa, kasashen yammacin duniya sun yi amfani da matakin soji don warware batun Somaliya, amma bai haifar da wani sakamako ba, illa ma, tsananta matsalar tsaro da rashin tabbas a kasar.

Manazarta na cewa, tun bayan da kungiyar Al-Shabaab ta yi mubaya'a ga Al-Qaeda, kungiyar ta fadada hare-haren ta zuwa kasashe da dama. Muddin ana son kawar da kungiyar,wajibi ne kasashen duniya su yi hadin gwiwa, tare da yin amfani da karfi tare da sauran kasashen waje, kuma ya zama wajibi a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

Kazalika, Neyabella da Muandewa sun bayyana cewa, ya kamata shugabannin addinai da sarakunan kabilu daban daban na Somaliya su taka muhimmiyar rawa wajen sassauta ga yanayin da ake ciki a kasar. A sa'i daya kuma, ya zama wajibi gwamnatin ta tashi tsaye don raya tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma, musamman ma samar da guraben ayyukan yi ga matasa, ta hakan ne, za a iya kawar da illar da kungiyar ta'addanci ta kawo ga matasa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China