in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa tsarin ba da hidimma ga tsoffi a duk fadin jihar Xinjiang
2015-07-27 10:54:27 cri

Sabbin alkaluman kididdiga na nuna cewa, ya zuwa yanzu, an kafa ayyukan ba da hidimomi ga tsoffi 1726 a jihar Xinjiang, wadanda suka kunshi gadaje 52183, inda ko wadanne soffi dubu daya suna iya samun gadaje 20.6.

Yanzu haka kuma an kusa kammala bullo da tsarin kula da tsoffi a dukkan birane da kauyukan jihar ta hanyar kula da tsoffi a gidajensu baya ga yadda za su rika samun hidimomi a unguwoyi da sauran hukumomi.

Kididdigar da hukumar kula da harkokin jama'a ta jihar Xinjiang ta bayar kan aikin kulawa da tsoffi a shekarar 2013 ta bayyana cewa, ya zuwa karshen shekarar 2013, yawan tsoffin da shekarunsu na haihuwa ya dara 60 zai wuce miliyan 1.3 a jihar.

A kokarin da jihar ke yi na fuskantar karuwar yawan tsoffi, gwamnatin jihar ta dukufa kan ayyukan kula da tsoffi kwarai da gaske, kuma ta zuba jari mai dimbin yawa domin kafa hukumomin ba da hidima ga tsoffi. A halin yanzu, an kafa irin wadannan hukumomi 829, da kuma unguwoyi 184 dake samar da hidimomi ga tsoffi a jihar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China