in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fama da matsalar hatsi mai tsanani a kasar Sudan ta Kudu
2015-06-30 13:58:38 cri

Kasar Sudan ta kudu ta fada cikin yakin basasa jim kadan bayan da ta samu 'yancin kai. A sakamakon rikice-rikicen da suka kunno kai a kasar, yanzu haka ana fuskantar mummunar matsalar karancin hatsi a jihar Upper Nile dake arewa maso gabashin kasar Sudan ta Kudu, lamarin da ya jawo hankalin kasashen duniya sosai.

Udier wani karamin kauye ne dake nesa da birane, kuma ya yi kama da gari a baya.

Madam Marijka Van Klinken masaniyar lafiya ce da kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa wato ICRC ta tura zuwa garin, ta bayyana damuwarta game da matsalar abincin da ake fuskanta a garin, ta ce,

"Matsalar ta yi tsanani a bana. A sakamakon yake-yake, an lalata kasuwani. Kafin yakin, ana iya samun kayayyaki daga babban birnin kasar, Juba da kuma kasar Habasha, amma yanzu ana fuskanar matsalar rayuwa a sakamakon hauhawar farashin kaya da yake-yaken ya haddasa. Baya da kayan abincin da aka jefawa jama'ar garin ta jiragen sama, mazaunan garin suna kuma cin tsirai ne kamar ganyen itace domin su rayu."

A kwanakin baya wakilin CRI ya isa garin a lokacin da ma'aikatan agaji na Red Cross ke rarraba kayayyakin abincin da aka jefawa mazauna yankin ta jiragen sama, wadanda suka hada da garin masara, dawa, abincin musamman na jarirai da kananan yara, da kuma irin shuka da kayan aikin gona.

Garin Udier da sauran yankunan dake kewayensa sun fama da yake-yake wadanda suka kawo illa ga harkokin cinikayya a jihar Upper Nile, wannan ya sa mazauna yankuna ba sa iya sayen irin shuka. Kana jama'a sun rasa gidajensu a sakamakon yakin, don haka ba su iya ci gaba da gudanar da harkokinsu na shuke-shuke. Ga mutanen da suke fama da matukar yunwa kuwa, abincin da kungiyoyin agaji suka samar musu kai tsaye ya fi hatsin da suka shuka kyau da inganci.

Lual wani mazaunin garin Udier ne, kuma ya yi rajista da kwamitin ICRC, inda ya karbi isasshen abinci a wannan karo, ya ce,

"Abincin da na karba zai wadatar da iyalaina har na tsawon wata daya, amma ga wadanda ba su yi rajista ba ko suka bar gidajensu don neman abinci ko suka kasa zuwa nan don karbar abinci, zai yi musu wuya nan gaba. Don haka, zan ba su abincin da na samu. Wannan al'ada ce da mazauna garinmu mu kan bi, idan ba mu yi haka ba, to wadannan mutane za su mutu."

Bayan da kasar Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai a watan Yuli na shekarar 2011, jam'iyyar SPLM ta zama jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar. Sakamakon rikicin da ya barke tsakanin kabilun kasar a kokarin raba madafun iko da neman mallakar albarkatun man fetur, ya sa jam'iyyar ta rabu gida biyu. Tun daga lokacin, kabilar Dinka da ta girma a kasar da kabilar Nuer ta biyu mafi girma a kasar sun yi yaki da juna.

Lual dan kabilar Nuer ne, kuma kungiyar da 'yan kabilarsa suka kafa na adawa da jam'iyyar SPLM da ke mulkin kasar Sudan ta Kudu. Amma a ganin Lual babu wasu manyan bambance-bambance tsakanin wadannan kabilu guda biyu.

Lual ya sha bayyanawa wakilin CRI cewa, ba ya kyamar 'yan kabilar Dinka. Yana da abokai 'yan kabilar Dinka da dama, a lokacin da yaki ya barke sun gaya wa juna cewa, ba za su yaki juna ba.

Ga Lual dan shekaru 26 da haihuwa, bai taba zama cikin kwanciyar hankali a rayuwarsa ba, ya bayyana cewa,

"An haife ni a cikin yaki, na girma a cikin yakin, kuma an haifi yarana a cikin yaki. Ba na kaunar yaki. Ina son gayawa shugabannin bangarori daban daban da yakin ya shafa cewa, abin da muke so a kasar Sudan ta Kudu shi ne zaman lafiya." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China