in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da ayyukan gina tashar samar da wutar lantarki mafi wahala na Afrika lami lafiya
2015-06-29 13:50:01 cri

A tsakiyar watan Yuni na wannan shekara ne, aka datse wani bangare na ruwan kogin Nilu domin gina tashar samar da wutar lantarki ta Karuma daga ruwan kogin da ya ratsa kasar Uganda dake gabashin Afrika, wannan ya nuna cewa, an kammala wani muhimmin aiki na wannan gagarumar tashar samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da karfin ruwa da kamfanin kasar Sin yake ginawa. Yanzu ga cikakken bayanin da abokiyar aikinmu Lami za ta kawo mana.

Tashar samar da wutar lantarki ta Karuma ta sha bambam da sauran tasoshin wutar lantarki, sabo da tana da wurin adana ruwa mai girma a karkashin kasa, shi ya sa, aikin gina ta ya fi wahala a Afrika.

Tashar samar da wutar lantarki mai yin amfani da karfin ruwa ta Karuma ta fi wadanda ke kasar Uganda girma, yawan kudin da aka kashe wajen gina ta ya kai dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 690, gwamnatin Uganda da bankin shige da fice na kasar Sin su ne suka dauki nauyin tattara wadannan kudade. Kamfanin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da karfin ruwa na kasar Sin ya fara gina tashar ce a watan Disamba na shekarar 2013, kuma zai kammala aikin gina ta kafin watan Disamba na shekarar 2018, tashar za ta zama tashar samar da wutar lantarki mai amfani da karfin ruwa mafi girma a gabashin Afrika.

Yadda ake datse ruwan da ke malala daga kogin na Nilu shi ne muhimmin aikin gina tashar wutar lantarki mai amfani da karfin ruwa. A matsayin daya daga cikin jerin tasoshin samar da wutar lantarki da aka gina a kan kogin Nilu, tashar Karuma ta sha banban da sauran irin wadannan tasoshi sosai, babu tsaunuka, ruwa ya kan malala daga kogin a kai a kai. Sabo da haka, aka gina wata ma'adanar ruwa a karkashin kasa da za ta rika samar da wutar lantarki ba tare da wata matsala ba

Shugaban kula da aikin gina tashar Karuma Song Yijun wanda ya taba gudanar da ayyukan gina tasoshin samar da wutar lantarki masu amfani da karfin ruwa a kasashen Ghana da Lesotho da kuma Uganda, yana ganin cewa, ana bukatar hako ramuka da dama, shi ya sa, gina tashar Karuma ke da wahala sosai. Ya ce,

"Tashar Karuma ta sha banban da sauran tasoshin samar da wutar lantarki matuka, mun hako ramin dake karkashin kasa domin janye ruwan da ke ciki, ta yadda za mu yi amfani da karfin ruwan. Tsawon ramin da muka hako ya kai kilomita kusan 30."

Wei Fuchun wanda ya fito daga birnin Hangzhou na lardin Zhejiang ya shafe sama da shekaru 30 yana ayyukan gina tasoshin samar da wutar lantarki masu amfani da karfin ruwa, kuma yanzu haka, shi ne mataimakin darektan da ke kula da aikin gina tashar ta Karuma, yana shiga babban ramin dake karkashin kasa tare da abokan aikinsa a kowace rana. Ya bayyana cewa, an yi amfani da fasahohi masu kyau na kasar Sin wajen gina dakin da aka haka a karkashin kasa mai hawa biyar.

Ya ce,

"Fadin dakin ya kai mita 21, tsawonsa ya kai mita 200, kuma tsayinsa ya kai mita 53. Muna nan mu na aikin haka hawa ta biyu na dakin, daga bisani, za mu haka hawa na uku, wadda shi ne hawa mafi muhimmanci, kuma za mu yi amfani da fasahohi mafi kyau na kasar Sin."

Tashar Karuma shi ne aiki mafi girma da kasashen Sin da Uganda suka yi cikin hadin gwiwa tun lokacin da suka kulla huldar diplomasiyya, yawan mutanen Uganda dake aikin gina tashar ya kai dubu 2 da dari 4. Mukasa Stuart Ahatur ke da shekaru 29 da haihuwa shi ne injiniyan dake kula da aikin tashar, ya kan duba ingancin ayyukan tashar a kowace rana tare da abokan aikinsa na kasar Sin, ya ce,

"Muna tantance ingancin katangar dakin dake karkashin kasa, idan mun gano wani kuskure ko wasu abubuwa marasa inganci, sai mu kira ma'aikata su sake dubawa."

An ba da labari cewa, tattalin arzikin Uganda na samun bunkasuwa cikin sauri, sai dai ana fama da karancin wutar lantarki sosai, amma bayan da aka kammala tashar Karuma, ana fatan tashar za ta biya bukatun sassa daban daban na kasar a fannin samar da wutar lantarki, kuma ana sa ran za a fitar da sauran wutar lantarkin zuwa kasashen dake makwabtaka da kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China