in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin kungiyar AU karo na 25
2015-06-15 10:48:58 cri

A jiya ne aka bude taron kolin kungiyar AU karo na 25 a birnin Johannesburg dake kasar Afirka ta Kudu, inda shugabanni ko wakilai daga kasashe membobin kungiyar AU fiye da 50 suka halarci taron don tattauna batutuwan bunkasuwa a Afirka, samar da 'yanci ga mata, tsaron yankin, kiwon lafiya da dai sauransu.

Taken taron na wannan karo bai bambanta da wanda ya gabace shi ba wato "samar da 'yanci ga mata da sa kaimi ga cimma burin raya Afirka nan da shekarar 2063", kuma za a tsara wani shirin samun bunkasuwa cikin shekaru 10 karo na farko don cimma wannan burin.

A shekarun baya baya nan, kungiyar AU ta kara yin imani ga makomar nahiyar Afirka a sakamakon yadda aka kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar Afirka, kuma AU ta gabatar da matakan kawo karshen dukkan yake-yaken da ke faruwa a yankin a shekarar 2020, da kawar da yunwa a shekarar 2025, kana an zartar da shirin raya nahiyar nan da shekarar 2063 a gun taron kolin kungiyar AU da aka gudanar a farkon bana, an ce za a yi kokarin kafa sabuwar nahiyar Afirka mai hadin kai, zaman lafiya da wadata a cikin shekaru 50 masu zuwa.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi jawabi cewa, nahiyar Afirka tana kan sabuwar hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki da ci gaba, kuma jama'ar Afirka suna da kyakkyawan fata ga shirin raya nahiyar nan da shekarar 2063. Kana Zuma ya ce, kamata ya yi kasashen Afirka su kara yin hadin gwiwa don kawar da matsalar tsaro tare da yakar ta'addanci da suka gallabi nahiyar Afirka.

Shugabar hukumar zartarwar kungiyar AU Nkosazana Clarice Dlamini-Zuma ta yabawa kasashen Liberia, Saliyo da Guinea da bangarorin da abin ya shafa bisa ga nasarar da suka samu ta yaki da cutar Ebola, ta ce, kungiyar AU za ta kyautata tsarin kiwon lafiyan kasashen da ke nahiyar don tinkarar cutar Ebola da AIDS ko kanjamau da dai sauransu.

Ta kara da cewa, ya kamata a koyi darasi daga tashe-tashen hankulan nuna kyamar baki da ya faru a kasar Afirka ta Kudu da hadarin nutsewar jirgin ruwan nan da ke dauke bakin haure da ya tashi daga Afirka zuwa Turai, a kuma gaggauta warware rikicin bakin haure da raya Afirka mai tsari bai daya don samar da yanayin hadin kai da bunkasuwa da zai jawo hankalin kwararru zuwa Afirka.

Shugaban kungiyar AU na wannan karo kana shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya jaddada muhimmancin masana'antu yayin da ake raya tattalin arzikin Afirka. Ya ce, Afirka tana dogara ne wajen fitar da albarkatun kasa wajen bunkasa tattalin arzikinta a cikin dogon lokaci, don haka ya kamata a kara darajar kayayyakin da ake fitarwa ta hanyar raya masana'antu don kara samun moriya daga albarkatun da Allah ya horewa kasashen nahiyar.

A gun taron, wakilai daga MDD da sauran hukumomin kasa da kasa da wakilai daga kasashe membobin kungiyar AU za kuma su ci gaba da tattauna yadda za a bada kariya ga yara mata, kawo karshen cin zarafin mata, tabbatar da 'yanci ga mata da dai sauransu.

Game da kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya da hana yaduwar cutar Ebola kuwa, an tsaida kudurin kafa cibiyar rigakafi da yaki da cututtuka ta Afirka a gun taron koli na kungiyar AU a karon da ya gabata. Kuma a taron kolin na wannan karo, shugabannin kasashe membobin kungiyar AU za su saurari rahoton cibiyar game da aikin hana yaduwar cutar Ebola.

Ban da wannan kuma, sakamakon karuwar ayyukan ta'addanci da ake fuskanta a kasashen Nijeriya, Somaliya, Mali, Kamaru da sauran kasashen Afirka, za a tattauna wasu muhimman batutuwa a taron kolin kungiyar AU na wannan karon, da za su shafi kara yin hadin gwiwar yaki da ta'addanci, da kafa rundunar sojan ko-ta-kwana ta Afirka wadda ake fatan za ta yaki ayyukan ta'addanci a nahiyar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China