in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 396 sun mutu a hadarin nutsewar jirgi a kogin Yangtze
2015-06-06 19:07:16 cri
Taron manema labarai da aka kira a yau Asabar dangane da hadarin nutsewar jirgin ruwa a kogin Yangtze ya shaida cewa, ya zuwa ranar Asabar 6 ga wata da rana, da misalin karfe 12, yawan mutane da suka mutu a hadarin ya karu zuwa 396, kuma ana ci gaba da neman fasinjojin jirgin a cikin dakunan jirgin da kuma karkashin ruwa da ma zuwa gabobin kogin.

A labarin da gwamnati ta bayar, an ce, jirgin na dauke da mutane 456, kuma kawo yanzu, 14 daga cikinsu ne kawai suka tsira da rayukansu, a yayin da ake cikin neman sauran mutane 46.

Har wa yau, wani jami'in soja ya bayyana cewa, tun bayan da aka fara gudanar da bincike cikin jirgin a Jumma'ar nan da ta wuce, an gano gawawwaki da dama. Domin kiyaye mutumcin matattu, an yi hankali sosai wajen kaurar da gawawwaki, domin kaucewar lalacewarsu. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China