in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gaggauta raya harkokin cinikayyarta da kasashen waje bisa dabarun aiwatar da manufar "Ziri Daya da Hanya Daya"
2015-05-28 17:24:06 cri

A kwanakin baya ne majalisar gudanarwar kasar Sin, ta fidda wasu shawarwari game da manufar gaggauta raya harkokin cinikayyar ta da kasashen waje, da nufin kara habaka cinikayyar kasar.

A kuma jiya Laraba 27 ga wata, mataimakin direktan sashen kula da cinikayyar kasashen waje, na ma'aikatar kasuwancin Sin Zhi Luxun, ya bayyana cewa idan aka kwatanta shawarwari da aka bayar a wannan karo, da wadanda suka gabata a baya, za a kara mai da hankali wajen aiwatar da manufar "zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21" wato "Ziri Daya da Hanya Daya" a takaice, don raya cinikayyar da Sin ke yi da kasashen waje。

Tun bayan Sin ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, musamman ma bayan da ta shiga hukumar cinikayya ta duniya wato WTO, kasar ta Sin ta bunkasa hamayyar ta da kasashen duniya, ta kuma tashi tsaye wajen canja salon raya wasu sana'o'i a kasashen duniya, tare da samar da babban ci gaba a fannin cinikayya da kasashen waje.

Bisa kididdiga, an ce yawan kudin da Sin ta samu ta hanyar shigowa da kuma fitar da kayayyaki a shekarar 1987, ya kai dalar Amurka biliyan 20.6, yayin da wannan adadi ya kai biliyan 4300 a shekarar 2014, inda ta zama kasa ta farko wajen fadin cinikayya da kasashen waje a duniya cikin shekaru 2 a jere.

Amma sakamakon sauyawar yanayin da ake ciki a gida da waje, matsalar cinikayyar wajen ta kasar Sin ta bullo, wato duk da yawan kudin da Sin ta samu wajen irin wannan cinikayya da kasashen ketare, abu ne mawuyaci a ce Sin tana ci gaba da samun karfi a fannin cinikayya, sabo da manyan ginshikai 3 da suka jibanci raya harkokin cinikayyar ta Sin sun canja. Mr. Zhi Luxun ya ce, "Na farko, kafin barkewar rikicin hada-hadar kudi na duniya, an samu bukatun cinikayya sosai daga kasashen waje, amma yanzu, an samu tafiyar hawainiya wajen karuwar irin wadannan bukatu. Sannan kuma, kayayyakin da ake bukata mu rika kerawa ko samarwa sun sauya, wato a da a kan bukaci kamfanonin ketare da ke kasarmu da suka samar da kayayyaki, amma yanzu kasashe masu ci gaba su kansu sun fara shiga wannan aiki. A karshe dai, duk da fiffikon da muke da shi a fannin gonaki da kuma makamashi, amma yanzu, sakamakon kayyade amfani da su kamar yadda ake yi a baya, fiffikon da muke da shi a wannan fanni ya ragu, kuma har yanzu ba mu samu wani sabon fiffiko na daban ba."

Har wa yau wani abun lura ma shi ne yawan kudin da Sin ta samu wajen cinikayyar ta da kasashen waje bai cimma burin da aka tsara ba cikin shekaru 3 da suka gabata, kana bisa sabuwar kididdigar da hukumar kwastam ta Sin ta bayar, an ce, yawan kudin da Sin ta samu a harkar cinikayya da kasashen waje a farkon watanni 4 na bana, ya kai RMB biliyan 7500, adadin da ya ragu da kashi 7.3 cikin 100 bisa na bara, hakan ya nuna cewa halin ciniki da waje da kasar Sin ke ciki bai samu kyautatuwa ba.

Game da wannan batu, manajan kamfanin sayar da na'urorin wutar lantarki mai suna Kaite dake birnin Hangzhou Ma Gaodong, ya bayyanawa wakilinmu cewa, idan aka kwatanta da abokan hamayar Sin a wannan fanni, irin fiffiko da Sin ke da shi a bangaren biyan kudaden kwadago ba shi da ingancin da ake fata."Kamar wadannan kaya da wayoyin lantarki, ba a bukatar fasahohi masu zurfi wajen yin su, kuma yanzu ana iya yin su a kasar Indonesiya, wadda ba ta buga haraji wajen fitar da su zuwa Amurka, yayin da ake bukatar haraji mai yawa da ya kai kashi 2.7 cikin 100 wajen fitar da su daga nan kasar Sin. Ban da wannan kuma, matsakaicin albashin dan kwadago na Indonesiya ya kai kudin Sin RMB 300 zuwa 500, yayin da wannan adadi ya kai RMB 3000 zuwa 5000 ga dan kwadago da ke nan Sin. Don haka akwai takara mai tsakani a fannin cinikayya da kasashen waje."

Yayin da Sin ke fuskantar raguwar fifikon cinikayya da kasashen waje, a hannu guda kuma, domin magance hakan, a kwanan baya, majalisar gudanarwar kasar ta fidda wasu shawarwari na kara karfin cinikayyar waje a kasar, inda mataimakin shugaban sashen kula da cinikayyar kasashen waje na ma'aikatar kasuwancin Sin Zhi Luxun ya ce, "Ya kamata a kyautata amfana daga kasuwanni na gida da na waje, da kyautata tsarin manyan kayayyakin da ake sarrafawa don cinikayyar kasashen waje, da sanya kwazo wajen samun sabon fiffiko a fannonin fasahohi, da tambari, da inganci, da aikin bada hidima, don kawo sabon kuzari da zai iya raya cinikayyar da Sin take yi da kasashen waje."

Haka kuma, Mr. Zhi ya ce, a cikin shawarwarin, an ce, ya kamata a hada manufar "Ziri Daya da Hanya Daya", da samun karuwar cinikin waje na kasar Sin bai daya, don cimma moriyar juna tsakanin kasar Sin da sauran kasashen dake manufar ta shafa. Ya ce,"Bayan da Sin ta gabatar da wannan shiri, wasu kasashen dake yankin sun zage damtse, wajen tsara manufofi don hadin gwiwa tsakaninsu, an kuma samu sakamako mai gamsarwa game da wasu ayyuka."

Bisa kididdiga, an ce daga shekarar 2001 zuwa shekarar 2014, matsakaicin karuwar yawan kudin cinikin da Sin ta yi da kasashen dake yankin "Ziri Daya Hanya Daya", ya kai kashi 22.2 cikin 100 a ko wace shekara, adadin da ya haura matsakaicin karuwar yawan kudin cinikin waje da kasar ta gudanar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China