in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Sin: aikin sintiri da jiragen saman yaki na Amurka ka yi a dab da tsibirin Sin ya sabawa doka
2015-05-28 11:08:08 cri

Bisa labarin da aka bayar, an ce kakakin ma'aikatar tsaron kasar Amurka ya jaddada manufar kasar sa na ci gaba da gudanar da sintiri, a dab da tsibirin Nansha na kasar Sin, a wani mataki na tabbatar da 'yancin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa.

Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana cewa kasar Sin, ba za ta taba lamuntar burin wasu kasashen ba, na fakewa da dalilan 'yancin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa, su keta ikon kare hakki, da kuma tsaron sararin sama da hanyoyin ruwa na sauran kasashe.

Hua wadda ta bayyana hakan a jiya Laraba, ta ce 'yancin zirga-zirgar jiragen sama da na ruwa, ba ya nufin baiwa kasashen waje damar keta ikon mallaka, da hakki, da kuma tsaron hanyoyin jiragen sama da na ruwan sauran kasashe.

Ta ce yarjejeniyar tsaron teku ta MDD ba ta bada izini ga wata kasa, ta tura jiragen sama da na ruwa su keta ikon mallaka, da hakki, da tsaron hanyoyin jiragen sama da na ruwan sauran kasashe ba. Ba kuma tare da la'akari da dokokin kasa da kasa ba.

Haka zalika kuma, Hua Chunying ta jaddada cewa Sin na da ikon mallakar tsibiran Nansha da sauran wadanda ke kewayensu, za kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukan gine-gine bisa doka a sassan yankunanta. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China