in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Burundi na kokari domin cibiyar CIRGL ta tsaya a Bujumbura
2015-05-28 10:54:24 cri

A jajibirin sanarwar taron kasa da kasa kan cibiyar kungiyar yankin manyan tafkuna (CIRGL) na cewa, za'a dauke cibiyarsa daga kasar Burundi dalilin rashin tsaro dake kamari a wannan kasa, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta mai da martani a ranar Laraba cewa, gwamnatin kasar za ta yi iyakacin kokarinta domin ganin ba'a gusa wannan cibiya ba daga kasar.

Gwamnatin Burundi tana da niyyar ci gaba da fadakar da kuma mai da hankali domin ganin cibiyar CIRGL ta tsaya a Bujumbura, in ji mista Daniel Kabuto, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar.

Haka kuma ya bayyana cewa, ma'aikatarsa ta samu labari cewa, babban taron Luanda na kungiyar CIRGL na ranar 18 ga watan Mayun bara ya bullo da wani kuduri bisa niyyar dauke cibiyar CIRGL daga kasar Burundi zuwa wata kasa daban, ministan harkokin wajen Burundi ya aike da wani sako ga takwaransa na kasar Angola domin nuna adawa kan wannan mataki.

Dalilin da aka gabatar a cikin wannan wasika shi ne cewa manufar kafa CIRGL ita ce ta karfafa zaman lafiya da tsaro a cikin kasashe mambobi, kuma wannan na nuna cewa, CIRGL na dukufa wajen neman hanyoyin warware matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu a kasar Burundi.

Ta hanyar tsayawa ne a Bujumbura tare da ma'aikatanta dake wurin, CIRGL za ta iyar taimakawa wajen kawo karshen rikicin da Burundi ke fuskanta a halin yanzu, in ji mista Kabuto. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China