in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iraki: Amurka ce ta haddasa habakar kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi
2015-05-28 10:50:24 cri

A kwanan baya, sakataren harkokin tsaron kasar Amurka Ashton Carter, ya zargi sojojin kasar Iraki da gaza taka rawar gani a yakin da ake yi da dakarun kungiyar IS, musamman yayin da dakarun kungiyar ke kokarin karbe muhimmin garin nan na Ramadi dake Irakin.

Game da wannan zargi wani masanin harkokin siyasar duniya daga jami'ar birnin Bagadaza Ibrahim Amali, ya ce Amurka ce ta haddasa habakar kungiyar ta IS cikin kasashen Iraki da Sham, da ma sauran kasashen dake yankin gabas ta tsakiya.

Shaihun malamin ya ce tsokacin da Mr. Carter ya yi bai dace da yanayin da ake ciki ba, duba da cewa galibin jama'ar kasar Iraki na ganin cewa manufofin neman mallakar duniya, da matsaya biyu da ake aiwatarwa game da yaki da ta'addanci ne sanadiyyar shigar IS cikin Iraki, shi ne kuma dalilin rashin cin nasarar yakin da ake yi da ta'addanci.

Amali ya kuma kara da cewa, tura sojojin da Amurka ta yi zuwa kasar Iraki a shekarar 2003, da hambarar da gwamnatin Saddam Hussein, da kuma goyawa wata jam'iyya baya, tare da rage karfin sauran jam'iyyun kasar, duka dalilai ne da suka haifar da karin sabani tsakanin al'ummun kasar mabiya darikun addinai daban daban. Hakan shi ne kuma musabbabin yaduwar ayyukan ta'addanci.

Don haka a cewar malamin, kamata ya yi kasar Amurka ta dauki nauyin kuskuren da ta tafka game da batutuwan da suka shafi kasashen duniya, ciki har da na yaki da ta'addanci. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China