in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara yin amfani da sansanin sojan kasa na kiyaye zaman lafiya na farko na kasar Sin
2015-05-27 14:51:46 cri

An yi bikin bude sabon sansanin sojan kasa na kiyaye zaman lafiya na farko na kasar Sin dake kasar Sudan ta kudu a jiya Talata, wato an kammala aikin shirya sansanin ke nan, kuma ya fara aiki a hukumance.

A safiyar jiya ne, jakadan kasar Sin dake kasar Sudan ta kudu ya buga ganga domin sanar da bude sansanin. Shugaban sansanin sojan kasa na kasar Sin Wang Zhen ya bayyana cewa, dukkan sojojin ba za su manta da nauyin da aka daura musu ba, kuma suna da niyyar gudanar da ayyuka daban daban musamman ma kare rayukan fararen hula, bisa jagorancin tawagar musamman ta MDD dake kasar Sudan ta kudu da kuma ikon da kwamitin sulhu na MDD ya bayar musu da dokar duniya, kana da yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen da suka tura sojoji wajen kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu.

Manzon musamman ta babban sakataren MDD Ellen Margrethe Loj ta yaba wa sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin sosai cewa, za ta ba da rahoto ga MDD domin gaya mata karfin da kasar Sin ta nuna wajen jibge sojoji cikin sauri, kuma ta yi imanin sojojin Sin za su kammala ayyukansu yadda ya kamata. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China