in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin ya yi tsokaci game da rahoton Amurka don gane da ayyukan soja da na tsaron kasar Sin
2015-05-09 16:51:02 cri
A Asabar din nan ne kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Geng Yansheng, ya gabatar da jawabi don gane da rahoton da Amurka ta fitar, game da yanayin bunkasuwar aikin soja, da tsaron kasar Sin na bana.

Cikin jawabin nasa, Mr. Geng ya ce rahoton da Amurka ta fitar, dangane da yanayin bunkasuwar aikin soja da tsaro a kasar Sin na shekarar 2015, ba bu kanshin gaskiya a cikin sa ko kadan, duba da yadda rahoton ya yi tsokaci game da barazanar da kasar Sin ke yi ga wasu sassa. A hannu guda rahoton ya kau-da-kai daga kokarin da Sin ta yi, na tabbatar da zaman lafiya a duniya, da ma na shiyyoyi, da raya dangantaka tsakanin rundunonin sojin kasar da na Amurkan.

Ya ce Amurka ta fidda rahoton mai cike da son rai, game da tsarin samun bunkasuwa cikin lumana, da manufar diplomasiyya na kasar Sin, da ma ayyukan kiyaye ikonta da kasar ta dauka a kudancin tekun Sin. Don haka Sin ta yi watsi da wannan rahoto.

Geng ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da nacewa ga hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da bin manufar diplomasiyya mai zaman kan ta. Kuma makasudin Sin na karfafa ayyukan tsaro, shi ne tabbatar da ikon mallakar cikakken yankin ta da tsaronta, a kokarin ta na tabbatar da samun ci gaba cikin lumana.

Bugu da kari rundunar sojin kasar na yin hadin gwiwa da ta sauran kasashen duniya a fannin tsaro cikin yakini, tana kuma taka rawar-gani, wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya. Kana dukkanin ayyukan da kasar ta Sin ke yi, na kiyaye ikon mallakar cikakkun yankunan ta na kasa, da na yankin teku, sun dace da doka, don haka a cewar Mr. Geng bai kamata a zarge ta kan hakan ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China