150506-Muhimmin-aikin-da-ke-gaban-sabbin-shugabannin-Najeriya-Sanusi.m4a
|
Duk da gudanar da zabukan kasar a ranakun da aka shirya, wasu na ganin cewa, za a tada hargitsi ko kuma ba za a wanye kalau bayan sanar da sakamakon zaben ba.
A yayin da kafofin watsa labarai da kungiyoyin addinai da na al'ummar kasar suka taka muhimmiyar rawa wajen gudanar zaben, ita ma hukumar zaben kasar mai zaman kanta (INEC) ta taka gagarumar rawa musamman amfani da na'urar tantace katin masu zabe (Card Reader) da a karon farko aka yi amfani da ita a zabukan kasar, lamarin da masu sa-ido a zaben daga sassa daban-daban na duniya suka ce ya rage magudi matuka da kuma tabbatar da sahihancin zaben.
Yanzu dai an kammala zabukan Najeriya inda Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya lashe zaben shugaban kasa da wasu jihohi da dama da kuma kujerun majalisun tarayya da na jihohin kasar.
Sai dai masana na ganin cewa,akwai jan aiki a gaban shugabannin da aka zaba, ganin yadda al'amura suka tabarbare a kasar kamar tsaro da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa kamar harkar wutar lantarki, ruwan sha da kiwon lafiya da ilimi da sauransu.
Bugu da kari abin jira a gani shi ne mutanen da sabuwar gwamnatin za ta nada a mukaman ministoci da sauran manyan mukamai da za su taimakawa shugaban kasar wajen tsoma kasar da al'ummarta daga halin da suke ciki.(Ibrahim/Sanusi Chen)